Jump to content

Joseph Ladipo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Joseph Ladipo
mutum
Bayanai
Jinsi namiji
Ƙasar asali Najeriya
Suna Joseph
Shekarun haihuwa 10 ga Yuli, 1941
Wurin haihuwa Jahar Ibadan
Lokacin mutuwa 9 Mayu 2013
Wurin mutuwa Jahar Ibadan
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Mamba na ƙungiyar wasanni Shooting Stars SC (en) Fassara
Coach of sports team (en) Fassara Shooting Stars SC (en) Fassara
Wasa ƙwallon ƙafa

Pa Joseph Ladipo[1] (ranar 10 ga watan Yulin,shekara ta alif ɗari tara da arba'in da daya 1941 - ranar 9 ga watan Mayun 2013) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Najeriya kuma manaja.[2]

A lokacin wasansa, Ladipo ya buga wasa a Shooting Stars har zuwa shekara ta 1973. Bayan ya yi ritaya, ya zama mataimakin kocin ƙungiyar, kafin daga bisani a ƙara masa girma zuwa kocin ƙungiyar farko a shekara ta 1977. Daga shekarar 1982 zuwa 1988, ya kasance manajan Leventis United. Sannan ya koma manajan Shooting Stars daga shekarar 1990 zuwa 1992.[1]

Ladipo shine shugaban kocin tawagar mata ta Najeriya a gasar Olympics ta bazara ta shekarar 2008. Ya kuma jagoranci Najeriya ta lashe gasar All-African Games na 2007,[3] kuma ta ƙare a matsayi na uku a gasar cin kofin matan Afirka ta 2008.[4][5]

Rayuwa ta sirri

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Ladipo a Ibadan, kuma ana yi masa laƙabi da Jossy Lad.[1] Ya rasu a ranar 9 ga watan Mayun 2013 a gidansa da ke Ibadan yana da shekaru 71.[6]

  1. 1.0 1.1 1.2 Samfuri:FootballDatabase.eu
  2. https://www.worldfootball.net/player_summary/joseph-lapido/
  3. "Coaches react to death of Jossy Lad". Vanguard. 9 May 2013. Retrieved 11 May 2018.
  4. Paul, Sam (10 October 2014). "AWC: Can Super Falcons Conquer Africa Again?". PM News. Retrieved 11 May 2018.
  5. "Nigeria/Ghana: 2008 African Women Championship - Super Falcons Begin Campaign Against Ghana Today". Leadership. Retrieved 11 May 2018.
  6. Sanni, Tunde (10 May 2013). "Nigeria: Ex-Falcons' Coach, Jossy Lad, Dies At 72". AllAfrica.com. Retrieved 31 December 2019.

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]