Jumoke Akindele

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jumoke Akindele
Speaker of the Ondo State House of Assembly (en) Fassara

27 Mayu 2015 - 19 ga Maris, 2017
Rayuwa
Haihuwa Ondo
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Karatu
Makaranta Jami'ar Obafemi Awolowo
Harsuna Turanci
Yarbanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Jumoke Akindele lauya ce a Najeriya kuma mace ta farko da ta fara zama kakakin majalisar dokokin jihar Ondo. Hon. Bamidele Oleyelogun ne ya gaje ta.[1]

Rayuwar farko[gyara sashe | gyara masomin]

An haifeta a Okitipupa, wani gari a jihar Ondo kudu maso yammacin Najeriya. Ta yi karatun firamare a St. John's Primary School a Okitipupa kafin ta ci gaba zuwa makarantar sakandaren ƴan mata ta St. Louis, Ondo inda ta sami takardar shaidar makarantar Afirka ta Yamma a 1981. Ta samu digiri na farko a fannin shari’a a jami’ar Obafemi Awolowo University, Ile Ife kuma ta yi aikin lauya na wasu shekaru kafin ta tsunduma cikin siyasa a shekarar 2006.

Harkar siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

A watan Afrilun 2007, ta yi takarar kujerar Mazaɓar, mazabar Okitipupa II amma ta sha kaye a hannun jam’iyyar adawa. Ta sake tsayawa takara ne a ranar 11 ga Afrilun 2011, kuma an zabe ta a matsayin ‘yar majalisar dokokin jihar Ondo, inda ta yi aiki a matsayin Shugaban Kwamitin Majalisar kan Ilimi kafin a zabe ta a matsayin Shugaban Majalisar. A ranar 27 ga Mayu, 2015, aka zabe ta a matsayin Shugaban Majalisar sakamakon rasuwar tsohon kakakin Samuel Adesina. Ta bar mukamin shugabancin gidan ne a cikin takardar murabus mai kwanan wata 20 Maris 2018. Jumoke Akindele ita ce mace ta farko da ta fara zama kakakin majalisar a jihar.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Kayode Alfred. "Jumoke Akindele calls the shots in Ondo Assembly". The Nation.