Khadija Bukar Ibrahim
13 ga Yuni, 2023 - District: Damaturu/Gujba/Gulani/Tarmuwa
11 ga Yuni, 2019 - District: Damaturu/Gujba/Gulani/Tarmuwa
11 Nuwamba, 2015 - 9 ga Janairu, 2019 ← Viola Onwuliri - Zubairu Dada →
ga Yuni, 2015 - District: Damaturu/Gujba/Gulani/Tarmuwa
ga Yuni, 2011 - District: Damaturu/Gujba/Gulani/Tarmuwa
ga Yuni, 2007 - District: Damaturu/Gujba/Gulani/Tarmuwa | |||||||||||||
| Rayuwa | |||||||||||||
| Haihuwa | 6 ga Janairu, 1967 (59 shekaru) | ||||||||||||
| ƙasa | Najeriya | ||||||||||||
| Karatu | |||||||||||||
| Makaranta |
University of Surrey (en) Padworth College (en) Headington Rye Oxford (mul) Queen's College, Lagos | ||||||||||||
| Sana'a | |||||||||||||
| Sana'a | ɗan siyasa | ||||||||||||
| Imani | |||||||||||||
| Jam'iyar siyasa |
All Progressives Congress All Nigeria Peoples Party | ||||||||||||
Khadija Bukar Abba Ibrahim An haife ta ne ran shida ga watan Janairun, shekarar alif ɗari-tara da sittin da shida (06-01-1966).[1]
Ƴar'siyasar Nijeriya ce, kuma ƴar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ce, tayi wakilci a majalisar wakilai House of Representatives daga mazabun Damaturu, Gujba, Gulani, da Tarmuwa dake Jihar Yobe a shekarar alif dubu biyu da sha shida (2016). An naɗa ta a matsayin ƙaramar ministan harkokin ƙasashen waje lokacin Shugaba Muhammadu Buhari, Kuma ta kasance ƴar majalisa a karo na hudu sannan ta kasance matar tsohon gomnan jihar Yobe wato Bukar Abba Ibrahim.
Muhimman Ayyuka da Tallafi ga Matasan Yobe
- Shirin Taimakon Matasan Mazaba (Fase III): A cikin wannan shiri, Hajiya Khadija ta raba kayan sana'o'i da kayan amfanin yau da kullum ga al'ummarta. Kayayyakin sun haɗa da:
- Babura masu ƙafa-uku guda 44
- Injin ɗinki guda 220
- Injin niƙa guda 220
- Zannuwa guda 1,000
- Bargo guda 1,000
- Gidan sauro guda 1,000
- Buhunan dawa, masara, wake, da sauran kayan abinci
- Katonin taliya da galan-galan maiɗin girki
2. Horon Ƙwarewa da Tallafin Kuɗi: Ta horar da matasa 400 a fannin fasahar sadarwa (ICT) tare da ba su tallafin Naira 150,000.00 kowanne domin fara sana'a. Wannan shiri ya samu yabo daga gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, wanda ya bayyana shi a matsayin ci gaba mai kyau ga yankin da ya fi fama da rikicin ƴan ta'adda.
3. Horon Sana'o'i tare da Gwamnatin Tarayya: A haɗin gwiwa da Cibiyar Gudanarwa ta Kasa (CMD), ta horar da matasa maza da mata 80 a fannin gyaran gashi da aski, tare da ba su kayan aiki domin fara sana'a.
4. Horon Noma da Tallafin Kuɗi: Ta horar da matasa maza da mata 160 a fannin kiwon kaji tare da ba su tallafin kuɗi domin fara sana'a.
Ayyukan Ci Gaban Al'umma
Baya ga tallafawa matasa, Hajiya Khadija ta gudanar da ayyukan ci gaban al'umma kamar:
- Gina rijiyoyi 28
- Gina cibiyoyin lafiya na mata
- Gina cibiyar wanke koda a asibitin koyarwa na jami'ar jihar Yobe
- Gina ajujuwa 10 da banɗakuna masu inganci
- Kafa haske akan hanyoyi
Tallafin Mata da Ayyukan Ci Gaba
1. Horon Sana'o'i da Tallafi: Hajiya Khadija ta shirya horo na musamman ga mata a fannin sana'o'i kamar gyaran gashi da aski, inda ta ba su kayan aiki da tallafin kuɗi domin fara sana'a. Wannan ya taimaka wajen ƙarfafa gwiwar mata su dogara da kansu.
2. Tallafin Lafiya da Ilimi: Ta kasance mai goyon bayan shirye-shiryen kiwon lafiya da ilimi ga mata da yara, musamman a yankunan da rikici ya shafa. Ta tallafa wajen wayar da kan mata game da rigakafin cututtuka kamar shan inna, tare da ba da gudummawa ga cibiyoyin lafiya da makarantu.
3. Goyon Bayan Mata a Siyasa: Hajiya Khadija ta kasance mai fafutukar ganin an ba mata damar shiga harkokin siyasa da shugabanci. A shekarar 2015, ta nemi kujerar mataimakin kakakin majalisar wakilai, tare da samun goyon bayan ƙungiyoyin mata da masu rajin daidaito tsakanin jinsi.