Jump to content

Khomeini

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Khomeini
1. Supreme Leader of Iran (en) Fassara

3 Disamba 1979 - 3 ga Yuni, 1989 - Ali Khamenei
Rayuwa
Cikakken suna سید روح‌الله مصطفوی
Haihuwa Khomein (en) Fassara, 17 Mayu 1900
ƙasa Iran
Mutuwa Tehran, 3 ga Yuni, 1989
Makwanci Khomeini Mausoleum (en) Fassara
Yanayin mutuwa Sababi na ainihi (Ciwon zuciya)
Ƴan uwa
Mahaifi Seyyed Mostafa Khomeini
Abokiyar zama Khadijeh Saqafi  (1929 -  3 ga Yuni, 1989)
Yara
Ahali Seyed Nooruddin Hindi (en) Fassara da Seyed Morteza Pasandideh khomeini (en) Fassara
Ƴan uwa
Karatu
Harsuna Farisawa
Larabci
Malamai Hossein Borujerdi (en) Fassara
Abu al-Majd al-Isfahani (en) Fassara
Sheikh Fazlollah Nuri (en) Fassara
Ɗalibai
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, maiwaƙe, shugaban addini, akhoond (en) Fassara, Malamin akida da mystic (en) Fassara
Muhimman ayyuka Forty Hadith (en) Fassara
Kashf al-Asrar (en) Fassara
Islamic Government (en) Fassara
Q5948537 Fassara
Kyaututtuka
Aikin soja
Ya faɗaci Juyin Juya Halin Musulunci
Iran–Iraq War (en) Fassara
Imani
Addini Musulunci
Ƴan Sha Biyu
Jam'iyar siyasa Islamic Republican Party (en) Fassara
IMDb nm0451776
imam-khomeini.ir
Khomeini
Hassan Khomeini -Ruhollah Khomeini -Ahmad Khomeini

WeImam Khomeini (R.A) An haife shi ranar ashirin ga watan Jimada al-Thani 1320 hijira Kamariyya, wadda ta yi daidai da 30 ga watan Shahribar 1281, hijira shamsiyya (24 ga watan Satumba shekarar 1902 miladiyya) aka haife shi a garin Khumain, wani gari da ke lardin tsakiyana Iran. Iyayensa dai mutane ne masu tsoron Allah, masana ilimin Musulunci waɗanda kuma suka fito daga zuriyar Nana Fatima al-Zahra (a.s) inda suka sanya masa suna Ruhullah al-Musawi al-Khumaini.[1]

Shi dai ya gaji iyaye da kakanninsa ne wadanda daya bayan dayansu suka dauki nauyin aikin shiryar da mutane da kuma neman ilmi.[2] Mahaifin mariganyin Imam Khumaini (r.a) shi ne Mariganyi Ayatullah Sayyid Mustafa Musawi, daya daga cikin malaman da suka yi zamani da Ayatullah al-Uzma Mirza Shirazi (r.a). (A bisa al'ada) mahaifin Imam Khumaini ya tafi birnin Najaf na kasar Iraki don karatun addini inda bayan ya kai matsayin ijtihadi (matsayin iya ciro hukunce-hukuncen shari'a daga mabubbuga) sai ya dawo gida wato garin Khumain ya ci gaba da shiryar da mutane a can. A lokacin Imam yana shekara biyar mahaifinsa ya yi shahada sakamakon harin da aka kai masa a hanyarsa ta zuwa garin Irak saboda irin nuna rashin amin cewar da yaki yi da zaluncin mahukunta na wancan lokacin. Bayan wannan kisan gilla, danginsa da mutanen garin Khumain sun fito don nuna rashin amin cewarsu, bayan haka kuma suka wuce zuwa birnin Tehran don isar da kukansu da bukatan a zartar da hukunci (kisasi) A kan wadanda suka aikata danyen aikin. Wannan kisan gilla da aka yi wa mahaifinsa ya sanya Imam (r.a) tun yana karami ya fahimci dacin maraici da kuma ma'anar shahada. Don haka mahaifiyarsa (Banu Hajar) ita ce ta ci gaba da kula da kuma tarbiyantar da shi, kasantuwar ita ma ta fito ne daga madaukakin gida don kuwa ita jika ce wa Ayatullah Khunsari (marubucin littafin Zubdatul Tasanif)Da kuma goggonsa (Sahiba Khanum). To sai dai lokacin da Imam ya kai shekaru 15 a duniya ya rasa irin wannan kulawa lokacin da wadannan masu kulawa da shi suka rasu.

Hijira zuwa kum, domin Kammala karatu da karantar da Ilimin musulunci

[gyara sashe | gyara masomin]
Imam Khomeini

Jim kadan bayan hijirar Ayatullah al-Uzma Hajj mallam Abdulkarim Ha'iri Yazdi, Allah Yayi masa rahama, zuwan sa birnin Kum a farkon shekara ta 1300 hijira shamsiyya (Rajab shekarar 1340), Imam Khumaini shi ma ya yi hijira zuwa makarantar Hawza ta Kum don ci gaba da karatunsa a wajen manyan malaman garin. Karatun dai ya hada da karasa karatun littafin Mutawwal wajen Mirza Muhammad Ali Adib Tehrani, da kuma karasa darasin "Sutuh" wajen Ayatullah Sayyid Muhammad Taki Khunsari da Ayatullah Sayyid Ali Yathrebi Kashani; da kuma fikihu wajen shugaban makarantar Hauzar Kum Ayatullah mallam Abdulkarin Ha'iri Yazdi (r.a).[3]

Bayan rasuwar Ayatullah al-Uzma Ha'iri Yazdi, a bisa bukata da matsin lamban Imam Khumaini da wasu manyan malamai na makarantar hauzar Kum, Ayatullah Burujerdi ya dawo birnin Kum don ci gaba da kula da makarantun Hawzan garin a matsayin shugaba. A daidai wannan lokaci kuwa ana ganin Imam Khumainin a matsayin daya daga cikin manyan malaman da ake iya komawa gare su a bangaren fikihu, Usul, falsafa, irfani da akhlak.

Shekara da shekaru, Imam Khumaini ya yi yana karantar fa fikihu, Usul, sufanci da akhlak a makarantun Hawza na Kum da suka hada da Makarantar Fa'iziyya, Masjid al-A'azam, Masjid Muhammadiye, Makarantar Hajj Mullah Sadik da kuma Masallacin Salmusi da dai sauransu. Har ila yau ya kuma karantar da fikihu da sauran ilmummukan Ahlulbaiti (a.s) a masallacin Shaikh al-Ansari (r.a) da ke Najaf na tsawon shekaru 14, inda a nan ne a karon farko ya bayyanar da ra'ayin gwamnatin Musulunci cikin silsilar darussan da yake bayarwa na Wilayatul Fakih.

Imam Khomeini (R.A) a fagen gwagwarmaya

[gyara sashe | gyara masomin]

Ruhin jihadi da gwagwarmaya a tafarkin Allah yana da tushe na akida da tarbiyya da kuma ta zamantakewa da siyasa duk tsawon rayuwar Imam Khumaini. Imam ya fara gwagwarmayarsa ne tun lokacin samartaka, kuma ya ci gaba da hakan a bangarori daban-daban na kyautata ruhi a bangare guda, a bangare guda kuma kan yanayi na siyasa da zamantakewar al'ummar Iran da sauran al'ummomin kasashen musulmi. Rikicin da ya faru a shekarun 1340-1341 hijira shamsiyya (1961-1962) kan (zaben) kananan hukumomi ya kasance babbar dama ga Imam wajen jagorantar yunkurin al’umma. Don haka, ana iya cewa, yunkurin gama-gari na malamai da al'ummar Iran na 15 ga watan Khordad 1342 (5 Yunin shekarar 1963) ya kebantu da wasu siffofi guda biyu su ne kuwa jagorancin Imam Khumaini da kuma riko da Musulunci, wanda hakan ya zamanto matakin farko na yunkurin al'ummar Iran wanda daga baya aka fi saninsa da sunan "Juyin Juya Halin Musulunci".

Yayin da yake bayani kan abubuwan da ya tuna dangane da yakin duniya na farko, duk da cewa lokacin da aka yi yakin yana da shekaru 12 ne a duniya, Imam Khumaini yana cewa: "Lalle ina iya tuna abubuwan da suka faru a yakukuwan duniya guda biyu…a lokacin ina karami ne amma dai na kan je makaranta kuma ina ganin sojojin tarayyar Sobiyeti a sansanin da muke da shi a nan (garin) Khumain. A yakin duniya na farko a wasu lokuta akan kai mana hare-hare ma". A wani waje na daban Imam Khumaini ya kasance ya kan ambato sunayen wasu daga cikin ashararan da suke fakewa da hukuma wajen kai hare-hare da sace kayayyakin al'umma, inda yake cewa: "Tun ina karami nake cikin yaki….muna cikin mamayan Zulkawa da kai hare-haren Rajab'ali ne duk da cewa mu ma muna da bindiga. Mu kan je kai dauki alhali a lokacin ina cikin shekarun samartaka na ne. Mun kasance mu kan gina ramukan fakewa a inda muke… mu kan shiga cikin wadannan ramuka muna fada da wadannan ashararai da suke son kawo hari da mamaye mu".

Imam Khomeini tare da wasu mutane

A bisa wasu hujjoji na tarihi an tabbatar da cewa gwamnatin Birtaniyya ne ta shirya da kuma goyon bayan juyin mulkin da Ridha Khan ya yi a ranar 3 ga watan Esfand 1299 hijira shamsiyya (1920). Duk da cewa an kawo karshen mulkin Kajariyawa da kuma rage karfin mulkin ha’inai da ashararai, to amma dai ya haifar da wani tsari na kama-karya da wasu ‘yan tsiraru ke mulkan mutanen wata kasa da tsara musu makoma, inda 'yan gidan sarautan Pahlawi suka maye gurbin ashararai.

A irin wannan hali nea, duk da irin musgunawa malamai da gwamnatin lokacin da 'yan amshin shatan Birtaniyya da wasu 'yan boko da aka saya suke yi, amma (malaman) sun tsaya kyam wajen kare Musulunci. A wannan lokaci, bisa gayyatar da malaman Kum suka yi masa, Ayatullah Hajj Shaikh Abdulkarim Ha'iri ya yi hijira daga garin Arak zuwa Kum. Bayan wani lokaci kuma sai Imam Khumaini, sakamakon irin kokarin da yake da shi da kuma gama karatunsa na share fage a garuruwan Arak da Khumain, yayi hijira zuwa birnin Kum don ba da tasa gudummawar wajen karfafa sabuwar makarantar Hawzar garin. Daga baya ya yi fice wajen karantar da ilmummukan fikihu, falsafa da sufanci.

Rasuwar Ayatullah Ha'iri a ranar 10 ga Bahman 1315 hijira shamsiyya (10 ga watan Janairun shekarar 1937) ta sanya makarantar Hawzar Kum cikin hatsarin rugujewa, sai dai wasu malamai masu sadaukarwa sun ba da ta su gudummawar wajen ganin hakan ba ta faru ba. Cikin shekaru takwas din da aka yi, kula da makarantar ta kasance ne karkashin kulawar manyan malamai irinsu Ayatullah Sayyid Muhammad Hujjat, Sayyid Sadraddin Sadr da Sayyid Muhammad Taki Khunsari. A daidai wannan lokaci, musamman bayan faduwar gwamnatin Ridha Khan, yanayi yayi kyau da ya ba da dama wajen sake samar da cibiyar marja'iyya. A lokacin babu wanda ya dace ya maye gurbin Ayatullah Ha'iri da kuma kare makarantar Hawza daga faduwa kamar Ayatullah Burujerdi. Wannan hukumci na nada Ayatullah Burujerdi ya samu goyon bayan daliban Ayatullah Ha'iri ciki kuwa har da Imam Khumaini. A daidai wannan lokaci Imam da kansa ya yi ta kokari wajen ganin Ayatullah Burujerdi ya dawo garin Kum don rike shugabancin makarantar garin.

Imam Khumaini, sanadiyyar irin sanya ido kan yanayin da al'umma da makarantar Hawzar take ciki, da kuma karance-karance litattafa, jaridu da mujallu da kuma ziyarar da yake kai wa Tehran da ganawa da manyan malamai irin su Ayatullah Mudarris, ya fahimci cewa hanya guda ta magance mummunan yanayin da ake ciki bayan rashin nasarar yunkurin tsarin mulki musamman bayan darewar mulkin Ridha Khan ita ce taka tsantsan din makarantar Hawza, da tabbatar da alaka ta ruhi tsakanin malamai da al'umma.

A wannan kokari da Imam yake yi na karfafa makarantar Hawza ne ya sa a shekarar 1328 (1949) bisa goyon bayan Ayatullah Murtadha Ha'iri suka tsara wani shiri na kawo canji inda suka gabatar da shi ga Ayatullah Burujerdi. Wannan shiri ya fuskanci amincewar daliban Imam da sauran daliban da suke da wayewa.

Sai dai ita gwamnatin ta yi kuskure, saboda a ranar 16 Mehr shekarar 1341 (8 ga Oktoba shekarar 1962) majalisar hukumar Asadullah Alam ta amince da cire wasu dokokin karamar majalisar kasa, kamar dokar da ta shardanta cewa dole ne dan takara ya zamanto musulmi, rantsuwa da Alkur'ani mai girma, sharadin mazantaka ga 'yan takara da masu jefa kuri'a. Babu makawa akwai wata boyayyiyar manufa cikin amincewa da barin mata su kada kuri'a (da hukumar ta yi), kamar yadda cire sharadin Musulunci da mazantaka shi ma da wata manufa aka yi shi, ita ce kuwa shigar da 'yan Baha'iyya cikin al'amurran gudanarwa da ba su manyan mukamai cikin gwamnati.

Kamar yadda muka nuna a baya, taimako da goyon bayan haramtacciyar kasar Isra'ila da fadada alakar Iran da ita na daga cikin sharuddan da Amurka ta kafa wa gwamnatin Shah matukar tana son goyon bayanta. Don haka ne ya zamanto dole a bar 'yan kungiyar Baha'iyya ta 'yan mulkin mallaka su kame manyan bangarorin gwamnati don cika wannan sharadi. Jin kadan bayan watsa wannan labari, Imam Khumaini da wasu manyan malaman biranen Kum da Tehran, bayan wata tattaunawa, suka sanar da rashin amincewarsu da dokar.

Imam Khumaini ya ba da gagarumar gudummawa wajen fallasa asiri da manufofin gwamnatin Shah da kuma bayyana hakikanin nauyin da ya hau kan malamai da makarantun Hawza cikin halin da ake ciki. Hakan ne ya sa aka samu wasu malamai suka aike da wasu wasiku na nuna rashin amincewa ga Shah da priminista Alam, hakan ya faranta wa al'umma rai. Amma wasikun da Imam ya aike wa Shah da priministansa sun fi na sauran malaman tsauri da kuma jan kunne. A cikin daya daga cikin irin wadannan wasiku, Imam yana cewa: "Ina sake muku nasiha da tsoron Allah da kuma bin tsarin mulki, sannan ku guji saba wa Alkur'ani da dokokin malamai da shuwagabannin musulmi da kuma watsi da dokokin kasa; kada ku sanya kasa cikin hatsari da gangan, idan kuwa ba haka ba, malaman Musulunci ba za su daina yin maganganu a kanku ba".

Haka dai wannan batu na dokar kananan hukumomi ya kasance nasara ga al'umma kana kuma lamari mai muhimmanci gare su, musamman ma ganin cewa sun fahimci siffofin mutumin da ya cancanci ya jagoranci al'ummar musulmi. Duk da wannan rashin nasara da Shah ya fuskanta, to amma Amurka ta ci gaba da matsa masa lamba wajen ci gaba da canje-canjen da zai ba ta damar cimma manufofinta. Don haka Shah a watan Dey 1341 (Janairun shekarar 1962) ya gabatar da jiga-jigan shirinsa na canji guda shida da kuma bukatar a gudanar da jin ra'ayin al'umma kansu.

Har ila yau Imam Khumaini ya sake bukatar maraja'ai da manyan malaman garin Kum da su zauna don tattaunawa kan halin da ake ciki da kuma yiyuwar sake kaddamar da wani sabon yunkuri.

A ci gaba da goyon bayan da mutane suke nuna wa Imam, al'umma sun kaurace wa bukukuwan "Nuruz" (sabuwar shekara) don nuna rashin amincewa da ayyukan gwamnati. A cikin sanarwar da Imam ya fitar kan hakan, ya ambaci "Farin Yunkuri" (White Rebolution) na Shah da sunan "Bakin Yunkuri" (Black Rebolution), sannan kuma ya tona asirin manufar Shah ta biyan bukatun Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila. A bangare guda kuma, Shah, wanda ya tabbatar wa Amurkawa cewa al'ummar Iran sun amince da canje-canjen da yake son yi don cimma manufofin Amurka da ya ba shi sunan "White Rebolution", ya fahimci cewa rashin amincewar da malamai suke yi gare shi zai haifar masa da matsaloli masu girman gaske.

A cikin hudubobi da jawaban da ya dinga yi a gaban jama'a, Imam Khumaini ya dora alhakin wannan zalunci a kan Shah, kamar yadda kuma yake kiransa da dan koran haramtacciyar kasar Isra'ila da kiran al'umma da su yi masa bore. A wani jawabi da ya gabatar a ranar 12 ga Farbardin 1342 (1 Aprilu shekarar 1963) Imam ya yi Allah wadai da shirun da malamai suka yi a garuruwan Kum, Najaf da sauran garuruwan musulmi kan wannan danyen aiki na gwamnatin Shah, yana mai cewa: "Lalle a yau shiru yana nufin nuna goyon baya ga wannan hukuma ta zalunci". Washegari kuma wato ranar 13 ga Farbardin 1342 (2 Aprilu shekarar 1963) Imam ya fitar da sananniyar sanarwar nan tasa mai suna "Kaunar Shah Wasoso Ne".

Haka nan idan ana son fahimtar irin tasirin da kalaman Imam suke da shi a zukatan masu sauraronsa da har suke iya fita su ba da rayukansu, to dole ne a dubi asali da kiran nasa yake da shi da kuma irin gaskiya ta hakika da ke tare shi.

Shekarar 1342 hijira shamsiyya (1963) ta fara ne da kin fitowar da al'umma suka yi don bukukuwan "Nurooz" (sabuwar shekara) sakamakon kiran da malamai suka yi, da kuma zubar da jinin mutanen da ba su ci ba su sha ba a makarantar Fa'iziyya da ke birnin Kum. A bangare guda, Shah ya dage sai ya aiwatar da shirinsa na kawo canjin da Amurka ta ke bukata, a bangare guda kuma Imam Khumaini ya dage wajen wayar da kan al'umma wajen tsayawa da fuskantar tsoma bakin Amurka cikin al'amurran cikin gidan Iran da kuma ha'incin Shah.

A ranar 14 ga watan Farbardin shekarar 1342 (1963), Ayatullah al-Uzma Hakim daga garin Najaf ya aike wa wasu manyan malamai da maraja'ai na Iran da wasika yana kiransu da yin hijira ta gaba daya zuwa garin Najaf. Wannan kira dai an yi ta ne da nufin kiyaye rayuwar malamai da makarantar Hawza.

Imam ya yi kunnen uwar shegu da wannan barazana, don haka sai ya aikewa Ayatullah Hakim amsar wasikar da ya rubuto yana mai ce masa yana ganin babu wata maslaha ta Musulunci cikin yin hijira ta gaba daya da barin Hawzar Kum haka nan.

Imam Khomeini

Cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 12 ga watan Farbardin 1342 (22 Aprilu shekarar 1963) a lokacin bukukuwan kwanaki arba'in na shahadar (daliban) Fa'iziyya, Imam Khumaini ya jaddada goyon bayan malamai da al'ummar Iran ga jagororin kasashen musulmi da na larabawa wajen fuskantar haramtacciyar kasar Isra'ila, kamar yadda kuma yayi Allah wadai da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Sarki Muhammad Ridha Pahlawi da haramtacciyar kasar Isra'ila.


YUNKURIN 15 GA KHORDAD (5 GA YUNI) Watan Muharram na shekarar 1342 yayi daidai da watan Khordad ne (Yunin shekarar 1963) don haka Imam Khumaini ya yi amfani da wannan dama wajen motsa mutane da fuskantar hukumar kama-karya ta Shah.

A yammacin ranar Ashuran ta shekara ta 1383 hijiriyya (3 ga Yunin shekarar 1963) Imam ya gabatar da wani jawabi mai cike da tarihi a makarantar Fa'iziyya wanda shi ne matakin farko na yunkurinsa na 15 ga watan Khordad (5 Yuni).

A cikin wannan jawabi, yayin da yake magana da Shah, Imam yana cewa: "Ya Shah ina maka nasiha! Ya kai mai girma Shah, ina maka nasiha da ka janye hannayenka daga wadannan ayyuka naka! Suna yaudarar ka ne. Ba na son in ga mutane suna cikin farin ciki da murna idan har suka yi waje da kai..ina kiranka da ka yi tunani kan abin da suke sa ka fadi…ka saurari nasihata. Mece ce alakar da ke tsakanin Shah da (haramtacciyar kasar) Isra'ila da har 'yan SABAK (jami'an tsaron Shah) suke cewa kada ku fadi magana kan Isra'ila? Shin Shah Ba'isra'ile ne?". Shah dai ya ba da umarnin gamawa da wannan yunkuri. Da farko jami'an tsaro sun kame da dama daga cikin magoya bayan Imam a daren 14 ga Khordad (4 ga Yuni), kusan asubahin washe gari kuwa da misalin karfe 3 na asuba darurrukan 'yan sandan da aka aiko daga Tehran sun kewaye gidan Imam da nufin kama shi a lokacin yana sallar dare. Don haka bayan kama shi sai suka wuce da shi cikin gaggawa zuwa Tehran inda suka fara tsare shi a wajen tsare mutane na 'Officer's Club' daga baya kuma da yamma suka wuce da shi zuwa gidan yarin Kasr na birnin. Da safiyar 15 ga watan Khordad labarin kama Imam ya yadu zuwa garuruwan Tehran, Mashhad, Shiraz da sauran garuruwa lamarin da ya sa aka samu irin yanayin da aka samu a garin Kum na boren jama’a. A cikin littafin da ya rubuta abubuwan da suka faru a rayuwarsa, wani na kurkusa da Shah Janar Fardoust ya bayyana yadda aka zabi jami'an tsaro na musamman bisa taimakon Amurka don kawo karshen wannan yunkuri, sannan kuma yayi bayani kan irin halin damuwa da dar-dar din da Shah, ministoci da jami'an gwamnatinsa, janar-janar da sojinsa da kuma 'yan SABAK suka kasance ciki a wancan lokacin, da kuma yadda Shah da jami'ansa suka ta ba da umarni ba kan gado don kawo karshen boren da jama'a suke yi. Bayan kwanaki 19 a gidan yarin Kasr, hukuma ta dauke Imam daga inda ake tsare da shi zuwa gidan yarin da ke barikin soji na Eshrat Abad.

Ana iya cewa ya zuwa wani haddi an cutar da wannan yunkuri sakamakon kama jagoransa da aka yi a ranar 15 ga Khordad da kuma kisan kiyashin da aka yi wa magoya bayansa. Shi kuwa Imam ya ki ba da hadin kai da amsa tambayoyin masu masa tambayoyi a inda ake tsare da shi yana mai nuna cewa ba sa da hurumin yi masa tambayoyi. Don haka a yammacin 18 ga watan Farbardin shekarar 1343 (1964) ba tare da wata sanarwa ba sai gwamnatin ta sake Imam da daukansa zuwa Kum. Jin wannan labari ke da wuya sai dukkan garin ya cika da bukukuwa da farin ciki, aka ci gaba da shirya bukukuwa a makarantar Fa'iziyya da sauran gurare har na tsawon ranaku. An gudanar da bukin shekarar farko ta tunawa da abin da ya faru a ranar 15 ga watan Khordad a shekarar 1343 da wasu bayanan hadin gwuiwa da Imam Khumaini da sauran maraja'ai suka fitar, da kuma wani bayanin na daban da makarantar Hawza ta fitar don girmama wannan rana da sanya mata sunan ranar zaman makomi ta gaba daya.

A wannan rana (ta 4 ga Aban), Imam Khumaini ya fitar da wata sanarwa inda yake cewa: "Ya kamata al'ummar duniya ta san cewa dukkan wata wahala da matsalolin da al'ummar Iran da na musulmi suke ciki daga Amurka ne, daga baki 'yan kasashen waje ne. Al'ummar musulmi dai ba sa kaunar dukkan bakin haure musamman ma Amurka. Don kuwa Amurka ce take goyon bayan (haramtacciyar kasar) Isra'ila da kawayenta. Amurka ce ta karfafa (haramtacciyar kasar) Isra'ila don mayar da musulmi marasa matsuguni..".

Nuna rashin amincewar Imam ga wannan dokar (ba da kariya ga ‘yan kasar Amurka a Iran) ta sake sanya Iran cikin yanayi na sabon bore da yunkuri a watan Aban shekarar 1343 (1964). Da asussubahin ranar 13 ga watan Aban 1343 (1964), jami'an tsaro na musamman da aka turo daga Tehran sun sake mamaye gidan Imam dake garin Kum, inda suka sake kama shi, kamar yadda ya kasance a shekarar da ta gabata, alhali yana cikin salla da addu'oi, suka wuce da shi kai tsaye zuwa filin jirgin saman Mehr Abad da ke Tehran da sanya shi cikin wani jirgin saman soji da daman yake jira sai garin Ankara na kasar Turkiyya. Da hantsin wannan rana, jami'an tsaron SABAK, cikin jaridun kasar, sun sanar da koran Imam saboda zargin barazana ga tsaron kasa. Duk da irin halin dar-dar da ake ciki sai da al'ummar birnin Tehran suka fito don yi zanga-zanga a kasuwar birni don nuna rashin amincewarsu da wannan aiki, sannan kuma aka rufe makarantun Hawza na wani tsawon lokaci kana kuma aka aike da wasiku ga kungiyoyin kasa da kasa da kuma maraja'ai.

Imam Khomeini tare da almajiran shi

Imam ya zauna a Turkiyya ne na tsawon watannin goma sha daya. A daidai wannan lokaci kuwa gwamnatin Shah ta yi kokari wajen ganin ta gama da sauran kurar bore ta gaggauta kaddamar da shirin nata da Amurka take son ta gabatar. Imam ya yi amfani da zaman gudun hijira ta dole a kasar Turkiyyan wajen rubuta da tsara shahararren littafin nan nasa mai suna 'Tahrir al-Wasila.


KORAR IMAM (R.A) DAGA TURKIYYA ZUWA IRAKI. A ranar 13 ga watan Mehr 1344 (13 Oktoba shekarar 1965) jami'an tsaro sun tura Imam da dansa Ayatullah Sayyid Mustafa Khumaini zuwa gudun hijira ta biyu wato daga Turkiyya zuwa kasar Iraki. Bayan isarsa birnin Bagadaza, Imam Khumaini ya kai ziyara zuwa hubbarorin tsarkakan Imamai (a.s) da suke garuruwan Kazimain, Samarra da Karbala, daga nan kuma bayan mako guda, Imam ya wuce zuwa sabon masaukinsa da ke birnin Najaf mai tsarki.

Shekaru sha ukun da Imam ya yi a garin Najaf (Iraki), duk da cewa babu matsin lamba na kai tsaye kamar yadda ya fuskanta a Iran da Turkiyya, sun fara ne cikin wani irin yanayi na nuna adawa da cutarwa mai tsanani daga wajen wasu malaman jeka na yi ka da ma'abuta son duniya da suka sanya tufafin ma'abuta addini da har ta kai ma, duk da irin hakurin da aka san shi da shi, a wasu lokuta ya kan fito ya yi magana kan irin wahalar jihadi da gwagwarmaya a wancan lokaci. To sai dai hakan ba su sanya ya ja da baya da barin wannan tafarki da ya zaba wa kansa ba.

Don haka ya fara karantar da fikihu a watan Aban shekarar 1344 (Nuwamban shekarar 1965) a masallacin Sheikh al-Ansari da ke Najaf duk kuwa da irin matsin lamba da adawar da ya dinga fuskanta, haka dai ya ci gaba da karantarwa har lokacin da ya yi hijira zuwa birnin Paris na kasar Faransa. Irin karfin ilmin fikihu da Usul da dai sauran ilmummukan Musulunci da Imam ya ke da shi ya sanya cikin karamin lokaci, duk da irin matsalolin da yake fuskanta, azuzuwansa sun kasance daga cikin mafi shahara da yawan dalibai a makarantun Hawzan Najaf.

Tun isowarsa birnin Najaf, Imam bai katse alakarsa da mujahidan da suke cikin Iran ba, ya kasance ya kan aika musu da sakonni da wasiku yana mai kiransu da su ci gaba da tsayin daka wajen kiyaye manufar wannan yunkuri na 15 ga watan Khordad.

Duk da irin yanayi mai tsanani da wahala da Imam Khumaini ya ke fuskanta a inda yake gudun hijira, to amma hakan ba su sa shi ya bar tafarkinsa na jihadi da fuskantar gwamnatin Shah ba. A kusan ko da yaushe yana ci gaba da sanya ruhin kyakkyawar fata da nasara a zukatan al'umma ta hanyar jawabai da sakonnin da yake aikewa da su ga mutanensa.

A ranar 19 ga watan Mehr, 1347 (9 ga Oktoba shekarar 1968) a wata ganawa da ya yi da wakilin kungiyar Fatah mai fafutukan 'yanto kasar Palastinu, Imam Khumaini ya bayyana mahangarsa kan matsalolin da duniyar musulmi ke ciki da kuma yunkurin al'ummar Palastinu. A yayin wannan ganawa, Imam ya ba da fatawar wajibcin kebance wani sashi na zakka da ba da shi ga 'yan gwagwarmayar Palastinu.

A farko-farkon shekarar 1969 rikicin da ke tsakanin gwamnatin Shah da gwamnatin Ba'athawa ta Iraki kan iyakan kasashen biyu na ruwa ya tsananta. Hakan ya sanya gwamnatin Iraki korar adadi mai yawa na Iraniyawa da ke zaune a kasar, kamar yadda kuma gwamnatin ta yi kokarin amfani da irin adawan da Imam yake yi wa gwamnatin Shah don cimma manufarta.

Shekaru hudu na koyarwar Imam da kuma irin kokarin da yake yi wajen wayar da kan mutane ya sanya an samu 'yan canje-canje a makarantun Hawzan birnin Najaf. A shekarar 1348 (1969) wannan yunkuri na Imam ya samu wasu sabbin magoya baya daga kasashen Iraki, Lebanon da sauran kasashen musulmi wadanda suka dauki yunkurin a matsayin abin koyi.


IMAM KHUMAINI DA CI GABAN GWAGWARMAYA (1350-1356 = 1971-77) A karshe-karshen shekarar 1971, kai ruwa ranan da ke tsakanin gwamnatin Ba'athawa ta Iraki da gwamnatin Shah ya tsananta lamarin da ya yi sanadiyyar korar dubban Iraniyawa da suke zaune a kasar. Nan take Imam ya aike da wasika zuwa shugaban kasar yana yin Allah wadai da wannan aiki sannan kuma ya sanar da aniyarsa ta barin kasar, sai dai hukumar ta hana shi saboda tsoron abin da zai iya biyo baya. A yayin bukukuwan zagayowar shekarar yunkurin 15 ga watan Khordad a shekarar 1975, dalibai a makatantar Fa'iziyya ta Kum sun gudanar da zanga-zangogi na kawanki biyu cikin makarantar suna masu rera taken "Aminci ya tabbata ga Khumaini", "Mutuwa a kan gidan sarautar Pahlawi". Duk da cewa hukuma ta haramta kungiyoyi da jam'iyyu masu adawa da ita sannan kuma da dama daga cikin ma'abuta addini da 'yan siyasa masu jihadi suna tsare a gidahen yari, amma duk da hakan kungiyoyi masu jihadin sun haifar da gagarumar hasara ga hukumar, hakan ne ya sanya jami'an tsaro (SABAK) suka fada wa makarantar da musguna wa dalibai musgunawa mai tsanani da kuma tsare su a gidajen yari.

Imam Khomeini tare da major javad

A ci gaba da ayyukansa na kiyayya da Musulunci, a watan Esfand 1354 (Fabrairun shekarar 1975), Shah ya canza kalandar (kwanakin wata) da hukuma take amfani da ita da ta fara daga hijiran Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya zuwa farkon mulkin mulukiyya Hakhamanshiyyawa. Imam Khumaini ya mayar da kakkausar martini ta hanyar fitar da fatawar haramcin amfani da wannan kalanda. Kamar dai yadda al'umma suka karbi fatawar haramcin shiga jam'iyyar Rastakhiz da Imam ya bayar, haka ma a wannan karon suka karbi wannan fatawa da hannu bibbiyu. Dukkan wadannan abubuwa biyu ana ganinsu a matsayin bugun hanci ga Shah. Hakan ya tilasta masa janye wannan sabuwar kalanda tasa a shekarar 1357 (1977).


KAMARIN JUYIN MUSULUNCI DA YUNKURIN AL'UMMA A 1356 (1977) Imam Khumaini wanda ya kasance mai sanya ido sosai kan abubuwan da ke gudana a Iran da sauran kasashen duniya, ya yi kokarin amfani da duk wata damar da ya samu. A watan Mordad 1356 (Augustan shekarar 1977), cikin wani sako da ya aika, ya bayyana cewar: "Bisa la'akari da yanayin cikin gida da waje, da kuma buga irin ayyukan zalunci da hukuma take yi a jaridun kasashen waje, hakan dama ce ga masana, 'yan jami'a da ke karatu a ciki da wajen kasa da kuma kungiyoyin Musulunci a duk inda suke da ya kamata su amfana da ita wajen fuskantar hukuma".

Shahadar Ayatullah Sayyid Mustafa Khumaini a ranar 1 ga watan Aban shekarar 1356 (1977) da kuma irin tarurrukan zaman makokin da aka shirya a Iran sun kasance abubuwan da suka sake motsa makatantun Hawza da al'ummar Iran wajen sake fitowa don fuskantar hukuma. Shi kuwa a nasa bangaren, Imam Khumaini ya bayyana wannan lamari (na shahadar Sayyid Mustafa) a matsayin wata boyayyiyar ni'imar Ubangiji, wanda hakan ya zamanto abin ban al'ajabi ainun. Gwamnatin Shah ta yi kokarin cin mutumcin Imam ta hanyar watsa wata makala ta cin mutumci gare shi cikin jaridar Ittila'at. Sai dai wannan karon ma shika ta koma kan mashekiya ne, don kuwa maimakon hakan sai ta kasance ummul aba'isin din boren al'umma a ranar 19 ga watan Dey 1356 (9 ga Janairu shekarar 1977) da nuna goyon bayansu ga Imam lamarin da ya yi sanadiyyar shahadar wasu dalibai ma'abuta jihadi da raunana wasu da dama a lokacin da jami'an tsaro suka fada musu. Duk da irin ayyukan zalunci da wuce gona da iri da gwamnatin Shah take yi a kan 'yan gwagwarmaya, sai dai duk da hakan hukumar ta gagara kashe wutan wannan bore. Imam yana ganin babu wani amfani wajen gwagwarmayar 'yan majalisa, jam'iyyun siyasa da karfin soji ba tare da goyon bayan al'umma ba, kamar yadda kuma yake ganin hanya guda da ta rage ita ce kaddamar da jihadi matukar Amurka ta yi tunanin shirya juyin mulkin soji.


HIJIRAR IMAM DAGA IRAKI ZUWA PARIS A wata tattaunawa da ta gudana tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen Iran da Iraki a birnin New York na Amurka, ministocin biyu sun yanke shawarar korar Imam Khumaini daga Irakin. Don haka a ranar 2 ga watan Mehr 1357 (24 ga Satumba shekarar 1978), jami'an tsaro suka mamaye gidan Imam da ke birnin Najaf mai tsarki, hakan dai ya fusata al'umman musulmi na kasashen Iran, Iraki da sauran kasashen duniya.

Don haka a ranar 12 ga watan Mehr (4 ga Oktoban shekarar 1978), Imam Khumaini ya bar birnin Najaf ya nufi kasar Kuwaiti, sai dai kasar Kuwaitin ta ki amincewa ya sligo kasar sakamakon matsin lamban gwamnatin Iran. Ganin haka ya sa wasu suka ba da shawarar a tafi kasar Siriya ko Labanon, to sai dai shi Imam Khumaini bayan shawara da dansa Hujjatul Islam Sayyid Ahmad Khumaini, ya yanke shawarar tafiya birnin Paris na kasar Faransa. Don haka Imam ya isa birnin Paris a ranar 14 ga Mehr shekarar 1357 (6 ga Oktoba shekarar 1978) inda aka saukar da shi a gidan wani Ba'iraniye a unguwar Noefel Le Chateau da ke wajen birnin.

A can ma mahukunta ba su barshi ba don bayan wani lokaci jami'an kasar Faransan sun zo wajensa da nufin sanar da shi mahangar shugaban kasar na lokacin kan zaman Imam a kasar suna masu sanar da shi cewa dole ne ya janye hannayensa daga harkokin siyasa. Imam Khumaini ya mayar da kakkausar martini ga wannan bukata ta su yana mai cewa hakan ya saba wa ikirarin riko da tsarin demokradiyyar da Faransan take yi, yana mai karawa da cewa ko da lamarin zai kai ne ya dinga yawo daga wannan filin jirgi zuwa wancan, ba fa zai bar wannan tafarki nasa ba.


Imam Khumaini, a watan Dey 1357 (Disambar shekarar 1978), ya kafa majalisar juyin juya halin Musulunci don share fagen kafa hukuma ta Musulunci da kuma dawowarsa gida. A dai dai wannan lokaci kuwa Shah yana ta shirin gudu ya bar kasar sakamakon yadda ya ga al'amurra suna ta ficewa daga hannunsa. Don haka kwanaki biyu da kafa majalisar shawara da tattaunawa don nema wa gwamnatin Bakhtiyar goyon baya, sai ya gudu ya bar kasar a ranar 26 ga watan Dey shekarar 1357 (16 ga Disamba shekarar 1978). Jin labarin gudun Shah ke da wuya, jama'a a duk fadin Iran sun fito kan tituna don nuna farin cikinsu.


DAWOWAR IMAM GIDA BAYAN SHEKARU 14 NA GUDUN HIJIRA Tun farko-farkon watan Bahman shekarar 1357 (1979) labarin shawarar da Imam ya yanke na dawowa gida ya yadu ko ina. Jama'a kuwa duk wanda ya ji wannan labari sai ya zubar da hawaye don murna, don kuwa abin da suke jira kenan har na tsawon shekaru 14, duk da cewa suna cikin damuwa kan tsaron lafiyarsa, don har zuwa lokacin gwamnatin jeka na yi kan Shah ita ce ke mulki, sannan ga kuma dokan ta bacin da ta kafa na ci gaba da aiki. Imam Khumaini ya riga da ya dauki matsaya ta karshe, don haka sai ya sanar da al'ummar Iran, cikin wani sako da ya aike musu, cewa yana son ya kasance tare da su a wadannan ranaku masu muhimmanci. Hakan ya sanya gwamnatin Bakhtiyar, bisa hadin gwuiwan Janar Haizer, suka rufe filin jirgin saman birnin Tehran sashin zirga-zirgan waje.

Imam Khomeini

Bayan wasu 'yan kwanaki, gwamnatin Bakhtiyar ta bude filin jirgin sama saboda gagarar da ta yi wajen jure wa wannan bore na al'umma. Daga karshe, a safiyar ranar 12 ga watan Bahman 1357 (1 ga watan Fabrairun shekarar 1979) Imam Khumaini ya dawo gida bayan shekaru 14 na gudun hijira. Irin gagarumar tarbar da al'umma suka yi masa ya kai matsayin da hatta kafafen watsa labaran yammaci sun gagara inkarin hakan, inda su da kansu suka ce mutanen da suka tarbi Imam Khumaini sun kai miliyan 4 zuwa 6.


Wafatinsa da rabuwa da masoya, haduwa da abin kauna Hakika Imam Khumaini ya isar da abin da yake son fadi da kuma cimma abin da yake son cimmawa tsawon rayuwarsa a aikace. Don haka a halin yanzu cikin tsakiyar watan Khordad 1368 (farko-farkon watan Yuni shekarar1989) yana ta kan shirye-shiryen ganawa da Abin kaunarsa da ya gudanar da dukkan rayuwarsa don neman yardarSa. Wanda ya kasance bai taba mika kai ga wani bayanSa ba, kamar yadda bai taba zubar da hawaye ba sai don Shi, sannan kuma dukkan wakokin irfanin da ya rera (ko rubutawa) sun kasance suna bayanin kan dacin rabuwa da Abin kauna da kuma shaukin da yake yi na saduwa da Shi. A halin yanzu da lokacin yake gabatowa, duk da cewa abu ne da masoyansa ba za su iya jurewa ba, ya rubuta cikin wasiyyarsa cewa: "Ina muku sallama 'yan'uwana maza da mata, cikin kwanciyar hankali da rai mai natsuwa da ruhi mai farin ciki da zuciya mai fatan falalar Allah, in kama hanya zuwa ga gidana na har abada. Kuma ina mai matukar bukatar addu'arku ta alheri. Sannan ina rokon Allah Mai rahama da jin kai Ya karbi uzurina na karancin hidima da kurakurai da gazawa. Kuma ina fata jama'a za su karbi uzurina cikin kowane karanci na hidima da kurakurai da gazawa, kuma su ci gaba da karfi tare da kakkarfar aniya..

Babban abin ban al'ajabin shi ne cewa tun kafin shekaru da rasuwarsa, Imam Khumaini, cikin wasu baitocin wake ya yi batun rasuwarsa cikin watan Khordad inda yake cewa: Shekaru suna wucewa abubuwa suna ta faruwa Ni kuwa ina sauraron nasara a tsakiyan Khordad

Daidai karfe sha daya da minti ashirin na dare ranar asabar 13 ga watan Khordad shekarar 1368 (3 ga Yuni shekarar 1989) lokacin saduwa da abin kauna ya yi. A daidai wannan lokaci ne zuciyar da ta haskaka zukatan miliyoyi da hasken Allah ta tsaya cak (ta bar aiki). A daidai wannan lokaci masoya Imam sun boye wata kamara (na'urar daukan hoto) a asibitin da yake kwance don daukan abubuwan da ke gudana da aikin da aka masa har zuwa lokacin saduwa da abin kauna. Don haka lokacin da gidan talabijin din Iran ya nuna halin kwanciyar hankalin da Imam ya ke ciki a lokacin, kai kace zukatan al'umma za su fashe saboda shaukin da ba za a iya siffanta shi ba.

A lokacin lebbansa cike suke da ambaton Allah, a daren karshe na rayuwarsa ma'abuciya daukaka a daidai lokacin da dantsensa yake daure da alluran da ake kara masa ruwa, amma sai ga shi ya mike don sallar dare da kuma karatun Alkur'ani mai girma. A daidai sa'oin karshe na rayuwarsa, ba abin da ake gani face kwanciyar hankali da nitsuwa ta Ubangiji yana mai ikirari da kadaitakan Ubangiji da imani da sakon Manzo (s.a.w.a) har lokacin da aka dauki ransa zuwa wajen Ubangijinsa. Wannan rasuwa da ta rura wutan bakin ciki a zukata. Lokacin da aka watsa labarin rasuwar Imam, kai ka ce wata gagarumar girgizar kasa ce ta faru, ko ina sai bakin ciki idanuwa kuwa a cikin Iran da sauran wuraren da aka san Imam kana kuma shiriyarsa ta shiga sai zubar da hawaye suke. Masoyansa sai fitowa suke suna dukan kawuka da fuskokinsu da alkaluma da duk wani irin bayani ya zaga wajen bayyana hakikanin abubuwan da suka faru da irin bakin cikin da ake ciki. Lalle mutanen Iran da sauran ma'abuta juyi suna da hakkin yin irin wannan kururuwa da tarihi bai taba ganin irin girma da tsananinsa ba, don kuwa sun rasa wani masoyi ne da ya dawo musu da mutumci da daukakan da suka rasa, sannan ya katse hannayen muggan shugabanni da 'yan mulkin mallakan Amurka da sauran kasashen yammaci daga kasashensu, sannan kuma ya raya Musulunci da hakkokin musulmi da mutumcinsu, ya kuma tsai da Jamhuriyar Musulunci, ya tsaya kyam a gaban karfin shaidan don fuskantar darurrukan makirce-makircensu na kawar da gwamnatin Musulunci da haifar da fitinar cikin gida da waje tsawon shekaru goma. Kamar yadda kuma ya jagoranci yakin kariya na shekaru takwas yana fuskantar makiyan da suke samun goyon bayan gwamnatocin gabashi da yammaci ma'abuta girman kai. Hakika al'umma sun rasa jagoransu abin kauna sannan kuma makomarsu na addini kana kuma mai kira zuwa ga Musulunci na hakika.

Mai yiyuwa ne mutanen da suka gagara fahimtar hakikanin wannan lamari su kasance cikin rudani lokacin da – gidan talabijin ya nuna - halin da mutane suke ciki yayin jana'iza da bisne jikin Imam mai tsarki. Mai yiyuwa ne su sha mamaki lokacin da suka ji labarin rasuwar mutane masu yawa da suka gagara jurewa wannan babban rashi don haka zuciyarsu ta tsaya cak ko kuma na faduwar wasu gomomin mutane sakamakon tsananin bakin ciki da dai sauran abubuwa makamantan haka da suka faru. Sai dai mutanen da suka san ma'anar kauna kana kuma zukatansu suka ta'allaka da shi cikin sauki za su iya fahimtar lamarin da kuma ganinsa ba a bakin komai ba. A hakikanin gaskiya al'ummar Iran sun kasance masu tsananin kaunar Imam Khumaini, don haka yayin zagayowar shekarar rasuwarsa suke rera taken: "Kaunar Khumaini kaunar dukkan abubuwa masu kyau ne".

A ranar 14 ga watan Khordad shekarar 1368 (4 ga watan Yunin shekarar 1989), majalisar kwararru (ta zaban jagora) ta gudanar da taronta, inda bayan da Ayatullah Khamene'i ya karanta wasiyyar marigayi Imam Khumaini da ya dauke sa'oi biyu da rabi, 'yan majalisar suka fara gudanar da tattaunawa da shawara kan wanda zai gaji Imam don zama jagoran Juyin Juya Halin Musulunci. Bayan sa'oi na tattaunawa, dukkan 'yan majalisar sun amince da zaban Ayatullah Sayyid Ali Khamene'i (wanda a lokacin shi ne shugaban kasa) a matsayin sabon jagora. Ayatullah Khamene'i dai ya kasance daga cikin daliban Imam Khumaini (r.a) na kurkusa kana kuma daga cikin fitattun mutanen da suka ba da gagarumar gudummawa a Juyin Juya Halin Musulunci kuma daga cikin wadanda suka taimaka nesa ba kusa ba wajen kaddamar da yunkurin 15 ga watan Khordad, wanda ya tsaya kafada-kafada da sauran mataimakan juyin da ba da gagarumar sadaukarwa duk tsawon yunkurin Imam Khumaini da kuma dukkanin abubuwan da suka faru daga baya.

Shekara da shekaru kasashen yammaci da 'yan amshin shatansu na cikin gida sun kasance cikin dakon wannan rana ta rasuwar Imam bayan sun yanke kaunar samun nasara a kansa. Sai dai farkawar al'ummar Iran da kuma saurin da majalisar kwararrun ta yi wajen zaban mutumin da ya dace da wannan matsayi na jagoranci da kuma irin goyon bayan da mabiya Imam suka yi wa zaben ta sanya makiyan cikin damuwa da kawo karshen mummunan fatansu. Don kuwa ba ma wai kawai juyin Imam bai zo karshe ba ne (kamar yadda makiyan suka so), face ma dai juyin ya sake bude wani sabon shafi ne na ci gaba da watsuwa da kuma karfi. Shin tunani, alheri da gaskiya suna iya gushewa?

A rana da daren 5 ga watan Yuni shekarar 1989 miliyoyin al'umma birnin Tehran da sauran al'ummomin da suka shigo garin daga garuruwa da kauyuka sun taru a babban wajen salla (musalla) na Tehran don yin ban kwana ta karshe da mutumin da ya dawo da mutumcin da daukaka (wa al'umma) a duniyar da take cike da duhu da zalunci ta hanyar yunkuri da juyinsa kana kuma ya watsa yunkurin komawa ga Allah Madaukakin Sarki da daukakar dan'Adam a duk fadin duniya.

Dukkanin abubuwan da aka yi a wajen jana'izar da hannun al'umma aka yi shi, cikin kauna da shauki. An dora jikin Imam mai tsarki a wani waje da kowa zai iya ganinsa yana rufe da koren kyalle tsakiyan miliyoyin masu juyayi, dukkansu cikin bakin ciki da zubar da hawaye alhali suna magana da Imaminsu cikin harshen da ya sawwaka ga kowa. Dukkanin hanyoyi da lungunan zuwa wajen sallar cike suke da jama'an da suke sanye da bakaken kaya don nuna bakin cikinsu, gidaje da shaguna kuwa duk an sanya musu tutocin juyayi da nuna bakin ciki, karatun Alkur'ani kuwa daga ko ina, masallatai, ofisoshi, ma'aikatu da gidaje sai tashi yake yi. Da daddare kuwa ko ta ina sai kyandir kake gani an kunna su don nuna alamun hasken da Imam ya zo da shi, duk sun haskaka wajen sallar da kewaye, alhali iyalai sun kewaye su (kyandir) suna kallon haskensu don tuntuni da irin hasken da jagoransu abin kaunarsu ya zo musu da shi.

Taken "Ya Husain" da masu juyayin suke rerawa alhali suna dukan kirji da kawunansu ya mai da yanayin wajen tamkar yanayin Ranar Ashurar da Imam Husaini (a.s) ya yi shahada. Bisa la'akari da cewa al'umma ba za su sake jin sautin Imam Khumaini dake cike da yanayin tunasar da mutum Ubangiji a Husaniyyar Jamaran ba, hakan ya kasance abin tashin hankali ga al'umma. Haka dai mutane suka ci gaba da zama a gefen jikin Imam mai tsarki duk tsawon dare har garin Allah ya waye, inda da sassafiyar ranar 6 ga Yuni shekarar 1989 aka yi masa salla karkashin limancin Ayatullah al-Uzma Golfaygani.

Babu shakka irin yawan al'ummar da suka fito don tarbar Imam Khumaini a ranar 12 ga watan Bahman shekarar 1357 (1 Fabrairu shekarar 1979) da kuma sake maimaita hakan a ranar jana'izarsa, duk suna daga cikin abubuwan mamaki na tarihi. Kafafen watsa labaran duniya sun tabbatar da cewa adadin mutanen da suka fito don tarbar Imam lokacin da ya dawo gida sun kai miliyan shida, amma wadanda suka fito don jana'izarsa sun kai mutanen miliyan tara. Hakan kuwa duk da cewa cikin wadannan shekaru goma sha daya na jagorancin Imam Khumaini kasashen Turai sun yi dukkan abin da za su iya wajen nuna adawarsu ga Jamhuriyar Musulunci da suka hada da kallafa mata yakin shekaru takwas da dai sauran makirce-makirce da ya sanya al'ummar Iran cikin mawuyacin hali na kunci da takurawa da kuma rasa abubuwan kaunarsu masu yawan gaske wanda a bisa dabi'a hakan zai sanya su gaji da kuma watsi da wannan juyi nasu, to sai dai ina hakan bai faru ba daga dukkan bangarori. Don kuwa al'ummar da suka tarbiyyantu a makarantar Imam Khumaini sun tasirantu da kuma imani da kalaminsa na cewa: "A duniya, gwargwadon girma da darajar manufa, gwargwadon karfin jurewa wahala, cutarwa, sadaukarwa da rashi na duniya ne".

Bayan da bisne jikin Imam mai tsarkin ya ci tura sakamakon yawan jama'a, gidan radiyo ya sanar da daga jana'izar har zuwa wani lokaci da za a sanar nan gaba don haka jama'a su koma gidajensu. Sai dai jami'ai sun riga da sun san cewa lokaci bayan lokaci jama'a za su ci gaba da zuwa wajen jana'izar ne, don haka dai aka daure aka gudanar da ita a yammacin wannan rana duk kuwa da irin wahalhalun da ake fuskanta. Wasu kafafen watsa labaran duniya ma sun nuna wani sashi na wannan jana'iza.

Imam Khomeini

Ta haka rasuwar Imam Khumaini, kamar rayuwarsa, ta kasance matakin farko na sabuwar wayewa da gwagwarmaya da kuma tabbatar da tafarki da ambatonsa har abada, don kuwa gaskiya abar tabbata ce matukar duniya tana ci gaba da wanzuwa.

Hanyoyin hadi waje

[gyara sashe | gyara masomin]

Karin Bayani An samo wannan bayanin ne daga shafin http://hausa.khamenei.ir Archived 2019-02-16 at the Wayback Machine

  1. "Ruhollah Khomeini | Biography, Exile, Revolution, & Facts | Britannica".
  2. Abrahamian, Ervand (1989). Radical Islam: The Iranian Mojahedin. I.B. Tauris. p. 20. ISBN 1-85043-077-2.
  3. Moin 2000, p. 22