Kisan gilla a Benisheik
| ||||
Iri | Kisan Kiyashi | |||
---|---|---|---|---|
Kwanan watan | 18 Satumba 2013 | |||
Adadin waɗanda suka rasu | 159 |
Kisan gilla na Benisheik ya kasance kisan kiyashi ne wanda da ya faru ranar 18 ga watan Satumban shekarar 2013 a Benisheik, jihar Borno, Najeriya. An kashe wasu mutane 161.[1][2] Ƙungiyar Boko Haram ce ta ɗauki alhakin kai hare-haren.[3]
Cikakkun bayanai
[gyara sashe | gyara masomin]Garin Benisheik, na tsakanin garuruwan Damaturu da Maiduguri a jihar Borno. An fara kai harin ne a ranar 18 ga watan Satumba. 'Yan tawayen sun isa birnin ne cikin ayarin motoci, sama da ashirin, sanye da kakin sojojin Najeriya da suka sata, Bugu da ƙari ɗauke da makaman kariya daga jiragen sama (anti-aircraft weapons).[4] Ana zargin mayaƙan na ƙungiyar ta'addanci ta Boko Haram ne suka kaddamar da harin domin mayar da martani ga dakarun da ke ƙoƙarin kare birnin.[4] Ƴan tawayen sun shiga birnin ne inda suka kona gine-gine da dama tare da kafa shingayen binciken ababen hawa a kan hanyar Damaturu zuwa birnin Maiduguri. An kashe direbobin wadannan shingaye, idan suka tabbatar mazauna jihar Borno ne, yayin da wasu kuma da alama sun samu damar barin shingen salin alin.[4]
Bayan kwana biyu da afkuwar harin, ƙungiyar Boko Haram ta ɗauki alhakin kai harin.[3]
Abubuwan da suka faru
[gyara sashe | gyara masomin]Kwana ɗaya bayan harin, jami’an jihar Borno sun ce adadin waɗanda suka mutu ya kai 87, kodayake suna ci gaba da neman sabbin gawarwaki.[5]
A ranar 22 ga watan Satumba Abdulaziz Kolomi, na hukumar kare muhalli ta jihar, ya ce an samu ƙarin gawarwaki 55, wanda hakan ya sa adadin waɗanda suka mutu ya kai 142.[5] A cewar majiyoyin ƴan sanda, an gano wasu gawarwaki 16 a Benisheik da kuma wasu 19 a tsakanin Maiduguri da Bamboa.[3] Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a jimilce mutane 161 aka kashe; Matafiya 142, sojoji 2, ƴan sanda 3 da ƴan kasa 14.[6][7][8]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Nigerian Islamists kill at least 159 in two attacks | Reuters". Archived from the original on 2014-11-10. Retrieved 2017-06-30.
- ↑ BBC News - Nigeria's Boko Haram unrest: Scores dead in Benisheik raid
- ↑ 3.0 3.1 3.2 "Les Boko Haram ont tué 159 personnes au Nigéria". i24 News. 21 September 2013. Retrieved 3 February 2020.
- ↑ 4.0 4.1 4.2 "Nigeria : au moins 87 morts dans une attaque de Boko Haram". Le Monde (in Faransanci). 19 September 2013. Retrieved 3 February 2020.
- ↑ 5.0 5.1 "Boko Haram commet un nouveau massacre dans le nord-est du Nigeria". JeuneAfrique (in Faransanci). 20 September 2013. Retrieved 3 February 2020.
- ↑ Larcher, Laurent (20 September 2013). "Attaque de Boko Haram dans la capitale du Nigeria". La Croix (in Faransanci). Retrieved 3 February 2020.
- ↑ Idris, Hamza (20 September 2013). "Nigeria: Benisheik Attack Death Toll Now 161". Daily Trust. Retrieved 3 February 2020.
- ↑ "Boko Haram a tué près de 160 personnes dans le nord du Nigeria". Reuters. 20 September 2013. Retrieved 3 February 2020.