Jump to content

Kofa:Zamantakewa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kofa:Zamantakewa
Wikimedia portal (en) Fassara

Zamantakewa[gyara sashe | gyara masomin]

Zamtakewa

Zamantakewa na nufin tarayyar ɗan Adam tsakaninsa da mutane, ƴan uwansa da abokansa, kamar daga lokacin da yake cikin ƙuruciyar sa har zuwa girmansa. Zamantakewa na farawa ne daga kuruciyan yaro ko yazama mai jin magana ko kuma mara jin magana, Sannan ya shiga samartaka har izuwa dattijantaka , Alaƙan mutum da sauran ƴan uwanshi ne ke nuna cikakkiyar ɗabi'ar mutum yayin da yake ma'amalantar su ta hanyoyin magana da aiki.

Wayewa[gyara sashe | gyara masomin]

wayayyu

Kalmar wayewa ta samo asali ne daga kalmar “Wayau” akan cema mutum wayayye ne kaɗai idan ya iya shiga cikin al’umma daban-daban masu banbancin halayya, ɗabi’u da kuma al’ada, ya shiga cikinsu ya zauna lafiya, kuma suka ji daɗin zama da shi Ma’ana yanada ɗabi'ar da zai iya tafiyar da su a bi sa tunaninsu da hangen nesan su.

Akan cewa mutum wayeyye idan ya iya sarrafa duk wani abunda da yazo gaba gareshi ko kuma haduwa da mutane maban banta ƙabila ko yare. Misali mutum ya zauna cikin hausawa, da yarbawa, da inyamurai, kuma alhali a cikinsu akwai mugaye da nagari da macuta da 'yan iska da masu hali mai kyau, yana a matsayin ɗan kasuwa, batare da ɗaya daga cikinsu ya iya cutar da shi ba ko shi ya cuce su. Kuma yana mai kyautata mu’amalarshi dasu, kuma suma suna masu kyautata mu’amalar su da shi. Wannan shi ake cema Zamantakewa ko wayewa, ko ace ma mutum ya waye.

Mutum yana zama wayeyye ne ta hanyar saukin fahimtar sa da kuma yawan adadin mutane ko wuraren da ya taba mu'amalanta ko shiga.

Rukunnan wayewa.[gyara sashe | gyara masomin]

 • Zama waje daya domin tattauna mahimman abubuwa ko wani abunda ke damun su
  Mu’amala tattausa: zamantakewa na wayewa na buƙatar tattausar mu’amala tsakaninka da kowa yayin cuɗanya dasu, amman kada ya kasance mutum yayi sanyi da yawa ta yanda kowa zai raina shi. Idan kana mu’amala karinga tattausawa, in aka tsananta maka na farko ka maida tattausan mu’amala har sai in an tsananta ne sai ka nuna tsayuwan dakan ka, domin kar a raina ka ko kuma a cuce ka.
 • Magana mai daɗi: Zamantakewa ta wayewa na buƙatar yin Magana mai taushi da daɗin ji a gurin kowa. In kana ma mutane Magana mai daɗi zasu dinga son mu’amala da kai domin sunsan cewa zasu ji daɗi a yayin Magana da kai kuma baza su ji haushi ko baƙin ciki ba. Idan mutum ya iya Magana da mu’amala mai kyau to iya wannan ma kaɗai ya wadatar da shi a zamantakewa. A ƙaurace ma yawan zagi da batsa, domin hakan ba wayewa ba ne kuma yana jawo zubewar mutunci.
 • Sutura mai rufe tsiraici da tsafta: Zamantakewa ta wayewa na buƙatar sanya kaya masu kyau, ba lallai sai suna da tsada ba, indai suna da tsafta to ya wadatar in kuma akwai hali a iya a siya masu tsadan, amman almubazzaranci da kuɗi koda kaya ba wayewa bane illa rashinta. Sannan a ringa ƙaurace ma yawan sa kayan da suka tsufa, domin hakan na kawo raini da ƙasƙanci,
 • Ilimi na Zamantakewa da na addini :zamantakewa ta wayewa na bukatar ilimi mai dunbin yawa na Zamantakewa dana boko dana addini. Idan mutum ya samu ilimi to yana kaiwa makura a fannnin wayewa, ta yanda baza’a a iya taba shi ba ta kowane fuska
 • Nuna soyayya da boye kiyayya
 • Yawan tunani da nazari

Akasin wayewa[gyara sashe | gyara masomin]

Yadda akasha wahala a baya kenan saboda rashin wayewa a duniya kafin zuwan yanzun

Akasin wayewa na nufin Ƙauyanci ko gidadanci ko tumasanci Mutum yakan rasa wayewa ne idan bai iya zama da wasu mutane wanda bana yankinshi ba, ko ba al’adarsu ɗaya ba, ko ba ɗabi’ar su ɗaya ba, ko Addini. Kowanne Yare, addini, jinsin mutane, masu ilimi da mara sa ilimi na ganin cewa sun waye a cikin zuƙatan su da maganarsu da suturarsu da halayyarsu.

Kuma haka al’amarin yake. amman inda matsalar take shine; a cikin dukkan jinsin mutanen da muka lissafa akwai wayayyu sannan kuma akwai gidadawa.

 • Misali akan wayayyu daga kowanne jinsi.
 • Bahaushe dan boko”:- Idan dan boko ya iya shiga mai kyau na ƙananan kaya, kuma ya iya Magana da mu’amala da waɗanda ba ƴan boko ba, Kaman misalin almajirai (ba masu bara ba) ɗalibai a musulunci da sauran jinsin mutanen gari. Ya mu’amalance su ma’amala mai kyau a fannin Magana da ɗabi’a To za’a ce masa ya waye kenan. Amman idan yayi tunanin cewa yan boko ne kaɗai suka waye, saboda haka bazai yi mu’amala da wasu ba sai yan boko to bai waye ba a cikin al’umma.
 • Ustazu ɗan islamiyya” Idan ustazu ya iya shiga mai kyau na manyan kaya, kuma ya iya Magana da mu’amala da wadanda ba ustazai ba, Kaman misalin Yan boko da sauran jinsin mutanen gari. Ya ma’amalance su mu’amala mai kyau a fannin Magana da dabi’a, to za’a ce masa yawaye kenan. Amman idan yayi tunanin cewa ustazai yan uwansa ne kadai suka iya Magana kuma suke da hali mai kyau, saboda haka bazai iya mu’amala da wasu ba sai ustazai to bai waye ba a cikin al’umma.

Abin lura[gyara sashe | gyara masomin]

wasu wayayyun mutane masu amfani da wayoyin hannu

Duk wanda yayi tunanin cewa jinsin da yake sha’awa ne kaɗai suka waye to bai wayeba. Sannan iskanci ko bariki ba wayewaba ne, ana kiranta da “Rashin wayewa” misali:- Karuwai da mashaya da yan-daba na wannnan zamanin sun ƙara halaka a cikin gidadanci ta hanyar tunanin cewa indai baka mu’amala da mata a fannin zina ko shaye-shaye, ko karinga nuna cewa kai mai ƙarfi ne indai hakan kayi ba to baka waye ba kwata-kwata. In suka zo cikin waɗanda basa aikata irin abinda suke aikatawa, sai su kasa zama dasu har su ce musu basu waye ba, suna kallan yan boko, da ustazai, da ma’aurata, da yan son zaman lafiya gidadawa. Alhali har yau babu wata ƙasa a duniya da aka taɓa samun karuwai ko mashaya ko yan daba wanda suka zama shahararrun mutunen arziƙi ba. Hasali ma sun manta da cewa karuwanci da iskanci da dabanci duk akan sune ake saka doka a sassan duniya domin kawar da su.