Koibla Djimasta
Koibla Djimasta | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Faransa Equatorial Afirka, 1950 | ||
ƙasa | Cadi | ||
Mutuwa | 30 ga Janairu, 2007 | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Larabci Faransanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Union for Democracy and the Republic (en) |
Koibla Djimasta (an haifeshi a shekara ta 1950- 30 ga watan Janairu, 2007)[1] ɗan siyasan Cadi ne daga ƙabilar Sara wanda ya fito daga yankin Kudancin Chari-Baguirmi.
Tarihin rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Kasantuwar sa mai gudanarwa, Djimasta ya riƙe mukamai daban-daban na majalisar ministoci karkashin Shugabanni Hissène Habré da Idriss Déby, [1] wanda ya fara da nada shi a matsayin Ministan Lafiya da Harkokin Jama'a a majalisar ministocin da Habré ya kirkira a ranar 21 ga watan Oktoba na shekarar 1982, jim kadan bayan hawarsa mulki.
Bayan hawan Déby kan karagar mulki da halatta jam'iyyun siyasa masu adawa, ya zama memba na Union for Democracy and Republic, wanda aka kafa a 1992, kuma ya kasance jigo a jam'iyyar, tare da Jean Alingué Bawoyeu. [2]
Mutuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Ya mutu ranar 30 ga watan Janairu, 2007
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 "Kwafin ajiya" (PDF). Archived from the original (PDF) on 2012-02-07. Retrieved 2021-06-03.
- ↑ Alan John Day, Political Parties of the World, (2002), page 95.