Komfuta

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Na'ura
subclass ofelectronic device, computing platform Gyara
influenced byMUSASINO-1 Gyara
studied bycomputer science Gyara
Dewey Decimal Classification004, 621.39 Gyara
Na'ura.
Na'urar tafi da gidanka.
Na'ura.
IBM PC 5150.jpg
IBM Thinkpad R51.jpg
CP NeXTstation.
Pdp-7-oslo-2004.jpeg

Komfuta da turanci computer, ana fassara ta da 'na'ura mai kwakwalwa. Komfuta na'ura ce da za'a iya bata umurni data aikata wani aiki daya danganci lissafi ko nazari kuma ta gudanar da aikin a dankankanin lokaci, kuma ana bata umurni ta hanyar abinda ake kira da turanci Programming. Komfutocin da ake kyerawa a yanzu suna da dama na iya yin ayyuka da aka tsarasu wanda ake kiransu da Programs wannan ne yasa suke iya yin aiki mai yawa a dan karamin lokaci.

Amfani da komfuta[gyara sashe | Gyara masomin]

Komfutoci ana amfani dasu wurin aiwatar da ayyuka a kamfani, masana'anta da kayayyakin da ake aiki a gidaje dasu. wadannan komfutoci sun hada da kananan kayayyaki har da manyansu, kamar abin dafa abinci na Microwave, Rimotin tsara TV, Robotics, na'urar komfuta' wayar hannu da sauransu. Komfutocin da aka kirkira da farko anyi sune dan taimaka wa mutane yin lissafi kawai, kamar 'abacus'. Sannan ansama cigaba a rayuwar Dan'adam ta yadda yafara kirkiran sabbin komfutoci dazasu taimakesa wurin yin ayyuka masu wahala da daukan lokaci. Na'urar da aka fara kyerawa na komfuta dake amfani da wutan lantarki sune wadanda aka kyerasu a lokacin yakin duniya na II. Komfutoci na zamani da ake yinsu ayanzu suna dauke da []injina]]n dake aiwatarwa da gudanar da ayyuka acikinsu, kamar shashin gudanarwa da ake kira da turanci central processing unit (CPU), da kuma wani bangare na kwakwalwan komfutar dake kula da ajiye abubuwan da aka sanya aciki. Shi dai fannin gudanarwa ta komfuta itace ke aiwatar da ayyukan daya danganci lissafi da nazarce nazarce da sauransu.

Fannonin komfuta[gyara sashe | Gyara masomin]

Akwai Fannoni daban daban dasuka hada komfuta, akwai fannin kayayyakin dake waje wato output devices da na ciki wato input devices, da kuma kayayyakin dake sanya aiki acikin komfutar da wadanda ake saukar da aiki dasu daga cikin komfuta. Wadannan sune; keyboards, mice, joystick, monitor screens, printers, touchscreen. komfuta nada matukar amfani a rayuwar dan-Adam.

Anazarci[gyara sashe | Gyara masomin]