Kumbwada
Kumbwada | |
---|---|
masarautar gargajiya a Najeriya |
Kumbwada wata masarautar karkara ce a yankin arewacin tarayyar Najeriya mai yawan al'umma kusan mutum dubu 33,000.[1]
Gwamnati da siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Kumbwada an san masarautar da tsarin da aka sani kawai na mulkin jaha da mata kaɗai ke yi kawai. A halin yanzu Kumbwada na ƙarƙashin Sarauniya Hajiya Haidzatu Ahmed da kotun ta. Tsohon tsarin na hana maza mulki a kan ƙaragar mulkin masarautar, a cewar mazauna yankin. An gaji sarautar sarauniya a ɓangaren mata a gidan, kuma diyar sarauniya Idris a yanzu ita ce magajiyar sarauniya.[1]
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]A shekarar 1958 da Yarima Amadu Kumbwada ya bayyana cewa yana son ya gaji sarautar Kumbwada bayan mahaifiyarsa sarauniya, nan take ya kamu da rashin lafiya, aka kore shi daga masarautar; bai dawo ba.[1] Kumbwada dai mata akalla shidda a jere sun a mulki tun bayan da Gimbiya Magajiya Maimuna ta Zariya; Sarauniyar karshe, kakar Sarauniya Hajiya, ta rasu tana da shekara 113.[2]
Tattalin Arziki
[gyara sashe | gyara masomin]Yawancin mutanen Kumbwada manoma ne.[1]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 Dixon, Robyn (2010-04-06). "No man dares sit on this Nigerian throne". Los Angeles Times. Kumbwada. Retrieved 2010-04-07.
- ↑ "No male rulers please -- there's a curse on them". Aminu Abubakar. Agence France-Presse. Archived from the original on 2012-10-05. Retrieved 2010-04-07.