Jump to content

Kurgwi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kurgwi

Wuri
Map
 8°46′N 9°18′E / 8.77°N 9.3°E / 8.77; 9.3
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin NajeriyaJahar pilato
Ƙananan hukumumin a NijeriyaQua'an Pan
Yawan mutane
Harshen gwamnati Turanci
Labarin ƙasa
Altitude (en) Fassara 218 m
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
kurgwi

Kurgwi gari ne, a yankin tsakiyar Najeriya. Ana samunsa a karamar hukumar Qua'an pan dake jihar Filato. Garin yana zaune ne a kan babbar hanyar Shendam - Lafia a kudancin jihar Filato.

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.


KAFUWAR GARIN

Kafin ƙarni na sha tara, garin Kurgwi babbar gwadabe ce na ayari-ayarin ƴan kasuwa, wannan gwadabe ce ta miƙa har cikin rairayin hamadar (Sahara) zuwa Timbuktu, Tripolitania da kuma Maghreb. Ƴan kasuwar wadanda ke kasuwancin bayi, dadawa, ƙirgi, gishiri, tufafi, gaɓu da sauransu, kan yada zango a wurin da yanzu ake samun garin na Kurgwi, a wancan lokaci, ba a nan matsugunin garin na Kurgwi yake ba. Bayan wasu shekaru, wannan zango na baƙi, ya rikiɗe zuwa wani yanki na zaman al'umma. Akasarin ƴan kasuwan, al'ummomin ƙabilu ne daban-daban daga arewacin Nijeriya kamar Hausawa, Kanuri, Fulani da sauransu waɗanda suka tadda ƙabilu ƴan asalin ƙasar.

Bayan wasu lokuta masu tsayi, an samu cudanya da musanyar al'adu tsakanin waɗannan baki da ƙabilu ƴan asalin ƙasar ta hanyar auratayya kasancewar baƙin ƴan kasuwa ne waɗanda ke yawo ba tare da mata ba, hakan ya sanya samun wata al'umma mai ruwa biyu da ake wa laƙabi da Abakwariga.

MULKI DA SARAUTA

Tun bayan mutuwar sarki Kokuwa cikin shekarar 1940, an samu gagarumin sauye-sauye sakamakon ɗare gadon sarautar garin da sarki Ibrahim Kyari yayi. Ibrahim Kyari, ɗan asalin ƙabilar Kanuri ne, kuma shine sarki na farko Musulmi. Duk da cewa a daidai wannan lokaci, duniya na tsaka da yakin duniya na biyu, amma Sarkin yayi kokarin haɗa kan kabilun daban daban dake garin ta hanyar gina Masallacin Juma'a na farko a tarihin garin kuma na biyu a yankin Jihar Filato na yanzu bayan wadda aka gina a garin Wase shekaru da dama a baya.

ZAMANTAKEWA

Gari ne da ya haɗa kabilu da dama wa'danda suka kaurato daga sassan Najeriya daban-daban tun karni na sha tara sakamakon bunƙasar kasuwanci kayayyakin kamar irinsu dadawa, kirgi, gishiri da kuma kayayyakin amfanin gona.

AYYUKAN KASUWANCI

Mafi shahara cikin ayyukan rayuwar al'umma shine noma. Al'umma mazauna garin na noma kayayyakin amfanin gona kamar doya, masara, shinkafa da sauransu. kuma harkar sufuri shine mafi shahara cikin ayyukan kasuwancin mazauna garin.

ILMIN BOKO

A cikin shekarar 1951 ne, Shendam NA ta samu nasarar gina makarantar ƙaramar firamare na farko a garin na Kurgwi bayan wasu yunkuri har sau uku da aka yi a baya waɗanda suka gaza yin nasara. Sannan kuma, cikin shekarar 1976 ne gwamnatin jihar Filato ta kafa makarantar sakandare na kwana a garin. A fannin ilimin boko mai zurfi, garin itace mazaunin Kwalejin share fagen shiga jami'a ta Jihar Filato wato CASRS. Kuma babban sakandare kwana na gwamnatin jihar dake hanyar Shendam, itace makarantar sakandare kwaya ɗaya na gwamnatin Jihar Filato a dukkanin faɗin ƙaramar hukumar Qu'a an Pan. Bayan haka, akwai wasu makarantun gwamnatin na Firamare da kuma makarantu masu zaman kansu.

SIYASA

Garin Kurgwi, gari ne mafi girma a yankin gundumar Kwang, itace mafi yawan al'umma sannan kuma itace na gaba wajen harkokin kasuwanci. Garin kuma an tsagata gida biyu a siyasance inda mazaɓu biyu ne ke cikin garin, wato Kurgwi East Ward da kuma Kurgwi West Ward.

SHUGABANCI

Tun cikin shekarar 1983 garin Kurgwi ke fama da rashin shuagabancin na sarauta tun bayan mutuwar sarki na ƙarshe wato Kyari.

KABILU

Kabilu mazaunan garin sun haɗa da ƙabilar Goemai waɗanda sune ƙabilar dake zaune a tsohuwar garin na Kurgwi. Sannan kuma akwai kabilu kamar Abakwariga ( Baƙi na farko kamar Hausawa, Kanuri, Fulani da sauransu.

MANYAN MUTANEN GARIN KURGWI

1.Farfesa Hamidu Garba Sharubutu- Nigeria Agricultural Research Council. Executive Director.

2. Sheikh Zakariya'u Yusuf- Religious Scholar.