Kwalejin Koyon Aikin Jinya da Ungozoma ta Adamu Adamu, Azare
Appearance
Kwalejin Koyon Aikin Jinya da Ungozoma ta Adamu Adamu, Azare | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | jami'a |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 2021 |
Kwalejin Koyon Aikin Jinya da Ungozoma ta Adamu Adamu, Azare kwaleji ce ta koyar da aikin jinya da ke garin Azare a karamar hukumar Katagum a jihar Bauchi a Najeriya. An kafa ta ne a cikin shekarar 2021 bayan Ministan Ilimi ya ƙaddamar da ita kuma an fara karatu a cikin ta ne a cikin shekara ta 2022. [1] A halin yanzu, kwalejin ta karɓi rukunin ɗalibanta na farko kuma yanzu haka suna tsakiyar gudanar da karatu.
Darusa
[gyara sashe | gyara masomin]Waɗannan su ne kwasa-kwasan da ake da su a kwalejin koyon aikin jinya da ungozoma ta Adamu Adamu Azare: [2]
- Ilimin Kulawa da Majinyata (Basic Nursing)
- Ilimin Aikin Unguzoma (Basic Midwifery)