Jump to content

Kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Imo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Imo
Bayanai
Iri cibiya ta koyarwa
Ƙasa Najeriya
Tarihi
Ƙirƙira 1978
imopoly.edu.ng

Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Imo babbar makarantar koyarwa ce a Umuagwo, Jihar Imo, Nijeriya.

An kafa ta a 1978 a matsayin Kwalejin Aikin Gona na Michael Okpara, Umuagwo kuma aka daukaka ts zuwa matsayin (Polytechnic) wanda aka sauya mata suna zuwa Kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Imo, (Imo State Polytechnic) Umuagwo a 2007. makarantar tana ba da kwasa-kwasan, horo da bincike a duk rassan Aikin Noma, Kimiyyar Gudanarwa, Injiniya da Kimiyyar Abinci. An tabbatar da makarantar don bayar da difloma ta kasa da kuma cancantar difloma ta kasa.

Kwalejin kere keren mai nisan kilomita ashirin da shida ne daga Owerri akan hanyar Fatakwal kuma tana da kadada dari uku da sittin. Kogin Otamiri ya ratsa kan iyakarta, yana mai da shi kyakkyawan yanayi don samar da aikin noma duk shekara ta ban ruwa.

Chinwe obajii ya kasance malami a wannan cibiya kafin a nada shi shugaban Ma’aikatar Ilimi ta Tarayyar Najeriya.

  • Jerin kwalejin ilimi da fasaha a Najeriya

1.  https://ng.opera.news/ng/en/education/e09f275987b7cb90861fb75edbc66941 Archived 2021-06-03 at the Wayback Machine


2. http://www.imopoly.edu.ng/


3. https://web.archive.org/web/20100920212241/http://nbte.gov.ng/downloads/ACCREDITATION_STATUS_OF_PROGRAMMES.pdf

Hanyoyin haɗin waje

[gyara sashe | gyara masomin]