Kwasi Etu-Bonde
Kwasi Etu-Bonde | |||
---|---|---|---|
7 ga Janairu, 2017 - District: Kintampo North Constituency (en) Election: 2016 Ghanaian general election (en) | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Vume (en) , 13 Oktoba 1968 (56 shekaru) | ||
ƙasa | Ghana | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Cibiyar Gudanarwa da Gudanar da Jama'a ta Ghana MBA (mul) : management (en) University of Ghana Bachelor of Science in Agriculture (en) | ||
Harsuna | Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da entrepreneur (en) | ||
Imani | |||
Addini | Kirista | ||
Jam'iyar siyasa | National Democratic Congress (en) |
Kwasi Etu-Bonde dan siyasar kasar Ghana ne kuma dan majalisar wakilai ta bakwai a jamhuriyar Ghana ta hudu mai wakiltar mazabar Kintampo ta Arewa a yankin Brong-Ahafo akan tikitin takarar jam'iyyar National Democratic Congress.[1]
Rayuwar farko
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Etu-Bonde a Vume a yankin Volta na Ghana.[2]
Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Etu-Bonde yayi karatu a GIMPA (SME, Development and Management) inda ya sami EMBA A 2004.[1]
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Etu-Bonde ɗan kasuwa ne kuma Shugaba na SKY-3 Investments Limited da Sustenance Agro Ventures da ke Kintampo.[2]
Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]A shekarar 2015 ya tsaya takara kuma ya lashe zaben fidda gwani na majalisar dokokin NDC na mazabar Kintampo ta Arewa a yankin Brong Ahafo na Ghana. Ya lashe wannan kujera ta majalisar dokoki a lokacin babban zaben Ghana na 2016.[2]
Rayuwa ta sirri
[gyara sashe | gyara masomin]Etu-Bonde na da aure da ‘ya’ya biyar. Shi Kirista ne.[2]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 "Parliament of Ghana".
- ↑ 2.0 2.1 2.2 2.3 "Ghana MPs - MP Details - Bonde, Kwasietu". www.ghanamps.com. Retrieved 2019-04-27.