Lawrence Ayo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Lawrence Ayo
Ɗan Adam
Bayanai
Bangare na Nigerian senators of the 4th National Assembly (en) Fassara
Jinsi namiji
Ƙasar asali Najeriya
Suna Lawrence
Sunan dangi Ayo
Wurin haihuwa Owo
Sana'a ɗan siyasa
Muƙamin da ya riƙe mamba a majalisar dattijai ta Najeriya da mamba a majalisar dattijai ta Najeriya
Ɗan bangaren siyasa Alliance for Democracy (en) Fassara

Lawrence Olawumi Ayo an zaɓe shi a matsayin Sanata mai wakiltar Ondo ta Arewa a jihar Ondo ta Najeriya a farkon jamhuriya ta huɗu ta Najeriya, inda ya tsaya takara a ƙarƙashin jam'iyyar Alliance for Democracy (AD). Ya fara aiki a ranar 29 ga watan Mayun 1999.[1]

An haifi Ayo a Owo, cikin Jihar Ondo.[2] Bayan ya hau kujerar sa a majalisar dattawa, sai aka naɗa shi kwamitin ɗa’a da gata na majalisar dattawa.[3] An naɗa shi a cikin kwamitin wucin gadi na Majalisar Dattawa don bincikar kasafin Kuɗi da karya kundin tsarin mulki da Shugaba Olusegun Obasanjo ya yi, to amma kuma a cikin watan Oktoban shekarar 2002 yana cikin mambobin kwamitin da suka ƙi sanya hannu kan rahoton ƙarshe tun da ba a gayyace su da su shiga shirye-shiryen sa ba.[4]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]