Shu'aibu Ahmed Abbas (an haife shi a ranar 2 gawatan Janairu shekara ta 1992), wanda aka fi sani da Lilin Baba, mawaƙin Najeriya ne, marubuci, mai rikodin, ɗan wasan fim kuma ɗan kasuwa.[1][2] Lilin Baba ya yi fice a masana’antar shirya fina- finan Kannywood saboda rawar da ya taka a fim ɗinsa na farko mai suna Hauwa Kulu.[3] An zabe shi a City People Entertainment Awards na 2018 Arewa Most Promising Music Act of the Year.[4] Ya lashe kyautar Arewa Best RnB Music Act of the Year 2019 a kyautar City People Entertainment Awards.[5]