Lucy Jumeyi Ogbadu
Appearance
Lucy Jumeyi Ogbadu | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 25 Satumba 1953 (71 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Ahmadu Bello |
Sana'a | |
Sana'a | Malami |
Lucy Jumeyi Ogbadu (an haife ta 25 Satumba 1953) kuma ƙwararriyar mai ilimin ƙwayoyin cuta ce ta Najeriya kuma ta yi aiki a matsayin Darakta kuma Shugaba ta Hukumar Bunkasa Fasaha ta Kasa (NABDA), da kuma cibiyar bincike ta kasa a ƙarƙashin Ma'aikatar Kimiyya da Fasaha ta Najeriya har zuwa karewar wa'adinta a shekarar 2018.[1]
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Kafin a nada ta Babbar Darakta ta NABDA a watan Nuwamba 2013, Ogbadu tayi karatu a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria na tsawon shekaru ashirin sannan daga baya ta koma Jami'ar Jihar Benue, Makurdi, har tsawon shekaru shida. A cikin shekarar 2002 an nada ta Daraktar Bincike da ci gaba wato NABDA kuma daga baya ta yi aiki a matsayin Daraktan Kasuwancin Bioentrepreneurship daga 2004 zuwa 2005.