Jump to content

Lucy Thoumaian

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Lucy Thoumaian ko Rossier de Visme

[gyara sashe | gyara masomin]
Lucy Thoumaian
Lucy_Thoumaian_at_International_Congress_of_Women1915_(22785230005)_(cropped)
Lucy Thoumaian
Rayuwa
Cikakken suna Lucy Rossier de Visme
Haihuwa Amiens (en) Fassara, Rossier de Visme 1980 Switzerland
ƙasa Armenia
Mutuwa Tarayyar Amurka, 1940 United States of America
Sana'a
Sana'a Mai kare ƴancin ɗan'adam da peace activist (en) Fassara
Employers League of Nations (en) Fassara
Lucy Thoumaian ita ma tana daga cikin wa'yanda suka halarci taron Majalisar Mata ta Duniya

(Ameniya: Լյուսի Թումայան; 1890 – 1940) yar Armenia ce mai fafutukar neman zaman lafiya da yancin mata. An kore ta daga Armeniya ta taimaka ƙirƙirar makaranta a Chigwell[1] ga Armeniyawa marayu. Ta buga takardar neman zaman lafiya kafin ta halarci taron mata a Hague a shekarar 1915. Bayan haka, ta fara aiki da Ƙungiyar Ƙasashen Duniya.

Majalisar Mata ta Duniya a 1915. Hagu zuwa dama:1. Lucy Thoumaian - Armenia, 2. Leopoldine Kulka - Austria, 3. Laura Hughes - Canada, 4. Rosika Schwimmer - Hungary, 5. Anika Augspurg - Jamus, 6. Jane Addams - Amurka, 7. Eugenie Hanner, 8. Aletta Jacobs - Netherlands, 9. Chrystal Macmillan - UK, 10. Rosa Genoni - Italiya, 11. Anna Kleman - Sweden, 12. Thora Daugaard - Denmark, 13. Louise Keilhau - Norway

Thoumaian an haife ta a Switzerland da sunan Rossier de Visme.

An kori ita da mijinta Reverend Farfesa Garabed Thoumanian daga Armeniya kuma suka zama gudun hijira a Biritaniya. A can, sun shirya gidan marayu da makaranta a Oakhurst a Chigwell don Armeniyawa a cikin 1906.

A shekarar 1911, ta halarci Babban Taron gudu na Duniya na Farko a Landan wanda farkon ƙoƙari ne na yaƙi da wariyar launin fata. Duk da kasancewarta gudun hijira daga Daular Usmaniyya ta rungumi wakilan Turkiyya a matsayin wata alama ta bukatar yin aiki tare.[2]

A shekara ta 1914, ta buga wani bayani na zaman lafiya wanda yake da taken "Yaki ne na mutum, dole ne mace ta koma". Ta ba da shawarar cewa mata su rika tarukan mako-mako har sai an warware takaddamar da ta haifar da yakin[3]

  1. https://www.british-history.ac.uk/vch/essex/vol4/pp38-41#fnn96
  2. https://books.google.com.ng/books?id=r5_47lZOMHQC&pg=PT397&redir_esc=y#v=onepage&q&f=false
  3. https://books.google.com.ng/books?id=1VWEjQu6rv8C&pg=PA91&redir_esc=y#v=onepage&q&f=false