Ma'aikatar Watsa Labarai ta Tarayya da Wayar da Kan Jama'a (Nijeriya)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ma'aikatar Watsa Labarai ta Tarayya da Wayar da Kan Jama'a (Nijeriya)

Ma'aikatar Watsa Labarai ta Tarayya da Wayar da Kan Jama'a ma'aikata ce a cikin Gwamnatin Najeriya. Ita ce ke da alhakin yaɗa muhimman bayanai masu muhimmanci da za su inganta da saukaka tafiyar da mulkin dimokuradiyyar Nijeriya a matsayinta na Gwamnatin Tarayyar, tare da inganta al’adu da yawon buɗe ido na ƙasar.

Gwamnatin Olusegun Obasanjo ce ta ƙirƙiro ma’aikatar a shekarar 1999. Daga baya aka rusheta a ranar 11 ga watan Janairun 2007, a wani mataki na sake fasalin da ya kai ga kafa ma’aikatar yaɗa labarai da sadarwa ta tarayyar Najeriya da ma’aikatar yawon buɗe ido da al’adu da wayar da kan jama’a ta tarayyar Najeriya.[1] Sai dai a shekarar 2015 gwamnatin Muhammadu Buhari ta sake kafa ma’aikatar, wanda ya haɗe ma’aikatun biyu wuri ɗaya.[2]

Ma'aikatar na ƙarƙashin jagorancin wani minista da shugaban Najeriya ya naɗa. Ministan na yanzu shine Mohammed Idris Malagi, wanda ya fara aiki a ranar 21 ga watan Agusta 2023.[3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Lohor, Josephine; Ezigbo, Onyebuchi (2007-01-11). "Nigeria: Obasanjo Relinquishes Petroleum Portfolio". AllAfrica. Retrieved 2023-08-31.
  2. "FULL TEXT OF PRESIDENT MUHAMMDU BUHARI'S DEMOCRACY DAY SPEECH – National Orientation Agency". National Orientation Agency – Change Begins With Me. 1 March 2018. Retrieved 7 October 2023.
  3. "Breaking: Mohammed Idris Malagi sworn-in as Nigeria's information minister". Blueprint Newspapers Limited. 21 August 2023. Retrieved 7 October 2023.