Mahmood Ahmadu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mahmood Ahmadu
Rayuwa
Haihuwa Lagos, 9 Satumba 1966 (57 shekaru)
Sana'a
Sana'a business executive (en) Fassara da ɗan kasuwa

Mahmood Ahmadu (an haife shi 9 ga watan Satumban 1966), ɗan kasuwar Najeriya ne. Shi ne wanda ya kafa kuma shugaban zartarwa na OIS, wanda kuma aka sani da Online Integrated Solutions Ltd.[ana buƙatar hujja]

Rayuwar farko da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Mahmood a Najeriya. Ya yi karatun MBA a Nasarawa State University. Ƙara karatunsa ya zo ne ta hanyar gudanarwa, IT da kuma kwasa-kwasan masana'antar sadarwa, inda ya yi amfani da waɗannan fasahohin wajen fara ƙananan sana'o'i masu sayar da kayayyaki da ayyuka.[1]

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

A farkon shekarun 1980, Mahmood ya samu gado daga mahaifinsa, wanda ya kasance yana zuba jari a kamfaninsa na farko da aka fi sani da A2A International Limited. Kamfanin ya bayyana shi a cikin waɗanda suka fara kasuwanci a GSM a Arewacin Najeriya. Ya ci gaba da inganta kasuwancinsa a cikin shekaru masu zuwa tare da faɗaɗa kasuwancinsa na gida da waje. Ya kuma ƙara wayar da kan jama’a kan muhimmancin ilimi tare da inganta harkar ilimi ta hanyar shirye-shiryen bayar da tallafin karatu.[1]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 https://www.outlookindia.com/