Maikanti Baru
Maikanti Baru | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Misau, 1959 |
Mutuwa | 29 Mayu 2020 |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Ahmadu Bello |
Sana'a |
Maikanti Kachalla Baru (an haife shi a watan Yulib shekarar 1959 - 2020) injiniya ne kuma tsohon shugaban Hukumar Dillancin Mai ta Nijeriya. Ya riƙe muƙamin ne daga watan Yuli na shekarar 2016 zuwa watan Yuli na shekarar 2019. Baru memba ne a Hukumar Injiniyoyi ta Nijeriya. [1]
Rayuwarsa da karatunsa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Baru a cikin Yulin shekarar 1959 a Misau, Jihar Bauchi. Yayi makarantar Kwalejin Gwamnatin Tarayya a Jos inda ya gama a shekarar 1978. Daga bisani ya wuce Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya inda ya samu digirin Injiniyanci a shekarar 1982. Har ilayau, Baru yana da digirin digir-gir akan kimiyyar injiniyanci ta komfuta wanda ya samu daga jami'ar Sussex dake a ƙsar Ingila..[2]
Aikin gwamnati
[gyara sashe | gyara masomin]Baru ya fara aikin gwamnati ne da wani kamfanin gidan rodi na Jos na kimanin shekara ukku daga shekarar 1988 zuwa shekarar 1991. A shekarar 1991 ne ya fara aiki da kamfanin mai na ƙasa NNPC a matsayin manajan injiniya. A kamfanin NNPC ya riƙe muƙamai da dama daga ciki harda Janaral Manaja na sashen Gas, muƙamin da ya riƙe daga shekarar 1997 zuwa shekarar 1999.
An naɗa Baru ne a matsayin babban Janaral Manaja na kamfanin NNPC a ranar 4 ga watan Yuli na shekarar 2016. Kuma yayi ritaya a ranar 7 ga watan Yuli na shekara 2019 bayan da aka naɗa Mele Kyari a matsayin sabon Janaral Manaja. [3]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "10 things to know about new NNPC GMD, Maikanti Kacalla Baru". Premium Times. Retrieved 17 August 2019.
- ↑ "Maikanti Kacalla Baru". African Refiners Association. Archived from the original on 25 July 2019. Retrieved 21 August 2019. More than one of
|archiveurl=
and|archive-url=
specified (help); More than one of|archivedate=
and|archive-date=
specified (help) - ↑ "Buhari appoints Mele Kyari as new NNPC GMD, seven COOs". Daily Trust. Archived from the original on 12 July 2019. Retrieved 21 August 2019. More than one of
|archiveurl=
and|archive-url=
specified (help); More than one of|archivedate=
and|archive-date=
specified (help)