Mele Kyari

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mele Kyari
Rayuwa
Haihuwa Najeriya, 8 ga Janairu, 1965 (59 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Kanuri
Karatu
Makaranta Jami'ar Maiduguri
Harsuna Turanci
Kanuri
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a soja da geologist (en) Fassara

Mele Kolo Kyari (an haife shi a 8 ga watan Janairun shekarar 1965) masanin ilimin kasa ne ,kuma dan kasuwar mai nena danyen da kuma Manajan Darakta na 19 (GMD) na Kamfanin Mai na Kasa wato Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC). Kafin wannan nadin, Kyari ya kasance Manajan Janar na Rukunin Man Fetur na Kamfanin Mai na NNPC da kuma wakilin Nijeriya na Kungiyar Kasashe Masu Fitar da Man Fetur wato Organization of Petroleum Exporting Countries(OPEC) tun daga shekarar 2018.

Farkon rayuwa da Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Kyari a ranar 8 ga watan Janairun ahekarar 1965 a garin Maiduguri, jihar Borno . Ya halarci Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Biu a Jihar Borno tsakanin shekarar 1977 zuwa shekarar 1982. A cikin shekarar 1987, ya sami digiri na farko a kimiyya (BSc) a geology fannin ilimin ƙasa da ƙasa daga Jami'ar Maiduguri. [1]

Ayyuka[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan ritayar Maikanti Baru daga kamfanin a ranar 7 ga watan Yulin shekarar 2019, [2] gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta nada Kyari a matsayin GMD na 19 na Kamfanin Mai na Kasa.[3] A shekarar 1991, ya shiga kamfanin NNPC Processing Geophysicist tare da Hadakar Bayanai na Ayyuka. A shekarar 1991, ya fara aikin sa da Sashen Nazarin Yanayin Kasa na Najeriya a matsayin Field Geologist. Ya yi aiki a matsayin mai binciken Geophysicist tare da National Petroleum Investment Management Services(NAPIMS) a shekarar 1998. A shekarar 2007, Kyari ya shugabanci Gudanar da Rarraba Yarjejeniyar Bayarwa a Sashen Kasuwancin Danyen Mai (COMD)[4]. A shekarar 2014, ya zama Janar Manaja, danyen mai na Gudanar da Hannun Danyen mai yayin da a shekarar 2015 aka daga shi zuwa mukamin Janar Manaja na Rukuni, COMD. Shi ne mutumin da ke kula da Buɗaɗɗun Gwamnati, shirin ya taimaka wa gwamnati ta bi diddigin mai siye da siyar da ɗanyen mai. A ranar 13 ga watan Mayu shekarar 2018, ya zama Wakilin Najeriyar Na Kasa a OPEC .[5][6]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Kasim, Sumaina. "(Profile) Mele Kyari, the New NNPC Helmsman". ThisDay. Retrieved 8 July 2019.
  2. "Baru sets new bar for new NNPC GMD Mele Kyari". P.M. News (in Turanci). 2019-07-07. Retrieved 2019-07-08.
  3. "Kyari take over from Baru as NNPC oga" (in Turanci). 2019-07-08. Retrieved 2019-07-08.
  4. Kasim, Sumaina. "(Profile) Mele Kyari, the New NNPC Helmsman". ThisDay. Retrieved 8 July 2019.
  5. Published. "Five things to know about new NNPC GMD". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 2019-07-08.
  6. "Breaking: FG appoints Mele Kyari, new chief executive of NNPC". Vanguard News (in Turanci). 2019-06-20. Retrieved 2019-07-08.