Maimunat Adaji

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Maimunat Adaji
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

5 ga Yuni, 2007 - 6 ga Yuni, 2011
Rayuwa
Haihuwa Najeriya, 1957
ƙasa Najeriya
Mutuwa 2019
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Nigeria Peoples Party
Peoples Democratic Party

Hajiya Maimuna Usman Adaji ko Maimunat Adaji (an haife ta a shekara ta alif ɗari tara da hamsin da bakwai 1957 ta rasu-2019) ‘yar siyasan Najeriya ce. An fara zabenta a matakin Majalisar Wakilai a shekara ta dubu biyu da uku 2003. An sake zaben ta a shekara ta dubu biyu da goma sha ɗaya 2011 a jam’iyyarANPP All Nigeria Peoples Party.

Rayuwa da siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Malama ce mai ilmantarwa wacce ta mallaki wata makaranta wacce ta kasance 'yar siyasa a Jamhuriyyar Najeriya ta huɗu . An fara zabenta a majalisar wakilai a shekara ta 2003.[1] A 2007 ta riga ta kasance aar shekaru talatin a matsayin siyasa a Kwama. Ita 'yar jam'iyyar All Nigeria Peoples Party ce (ANPP) kuma har yanzu ana zaben ta a wani yanki wanda gaba daya mai goyon bayan jam'iyyar People's Democratic Party (PDP) ce.[2] Adaji ta kasance mataimakiyar shugaban kwamitin harkokin cikin gida karkashin jagorancin West Idahosa . [3]

A shekara ta 2011 aka zabe ta ta zama 'year majalisar wakilai a shekara ta 2011. Sauran matan da aka zaba a wannan shekara sun hada da Suleiman Oba Nimota, Folake Olunloyo, Martha Bodunrin, Betty Okogua-Apiafi, Rose Oko da kuma Nkoyo Toyo .[4]

Rasuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Adaji ta rasu a shekarar 2019, tana da shekara 62.[4]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Celebrities 28 04 13". Issuu (in Turanci). Retrieved 2020-05-05.
  2. Dambatta, Nasiru (5 July 2003). "Nigerian Men Will See Political Changes - Interview: Hon. Maimuna Adaji". AllAfrica. Retrieved 4 May 2020.
  3. "HOUSE OF REPRESENTATIVES COMMITTEES - 2007" (PDF). Legislative Digest. 1 (11): 9–11. August 2007.[permanent dead link]
  4. 4.0 4.1 "Women who will shape Seventh National Assembly". Vanguard News (in Turanci). 2011-06-06. Retrieved 2020-05-03.