Jump to content

Mala`iku

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mala`iku

Mala`iku halittu ne da Allah S.W.A ya halitta daga haske , daya ana kiranshi da mala`ika da yawa kuma ana kiransu da mala`iku, mala`iku ba maza bane kuma ba mata bane su, saboda basu da al`aura ko sigar jinsi , sannan basa cin Abinci kuma basa shan Abunsha haka ma basa bawali ko bayan gida, basa haihuwa kamar Mutum ko Aljan ko Dabbobi hallitar su kawai Allah yake yi, suna da fukafukai, saidai wasu sunfi wasu yawan fukafuki, suna tashi sama Kaman tsuntsaye, Aljanu da Dabbobi na iya ganinsu amman mutum baya ganinsu kwata-kwata, sai dai yana iya ganin su a sigar Mutum kamar yanda Sahabbai suka ga Mala`ika Jibril a sigan Mutum lokacin da yazo ya zauna a majalisin Annabi har ya tambaye shi akan Imani da Tashin kiyama da Alamomi Ta. kowanne jinsin mala`iku nada aikin da Alla ya basu su ringa aiwatarwa, kuma ya sanya su sun kasance jinsi-jinsi daban-daban, dukkan mala`iku masu biyayya ne ga Allah bisa ga abinda ya basu umurni, basa saba masa, wasu sunfi wasu girma, wasu sunfi wasu yawan fukafuki, wasu kuma sunfi wasu daraja. Wasu mala`ikun a duniyan nan namu Allah ya halicce su kuma ya ajiye su anan ta hanya basu aikin da zasuyi. Wasu kuma a Lahira suke tun farko, wasu ma a wasu guraran suke inda bawanda ya san gurin Sa 'anan Allah S.W.AYana ta halittan su har ranan tashin Alkiyyama.[1][2][3][4][5][6][7][8]

Zantuka akan mala`iku

[gyara sashe | gyara masomin]

Akwai mala`ikan dake kawo wahayi shine Mala`ika Jibril dukkanni Manzannin Allah sun shi kuma sun taba ganin shi amman a sigan Mutum shine malamin duka Manzanni da Annabawa. Akwai mala`ikan dake kula da busa kahon Tashin alkiyama tinda Allah ya halicce shi yana rike da kahon jira kawai yake yi Allah ya ace masa ya busu. Baya Magana baya komai kawaia tsaye yake yana jiran a bashi umurni, akwai mala`ikan mutuwa mai daukan ran Mutane kullun yana taba mutum sau saba`in yana mai ne man izinin daukan ransa , baya murmushi ko dariya ,kuma kullum yawo yake yi a cikin mutane yana daukan ransu da izinin Allah, akwai mala`iku a cikin wuta wadanda ba suda tausayi ko jin kai ,aikin su shine azabtar da yan wuta. Akwai mala`iku biyu a hugu da daman dan adam suna rubata aikinshi na alheri dana sharri. Dadai sauransu. [9]

Sunayen Mala`iku

[gyara sashe | gyara masomin]

Wannan dai-daikun suna ne da Allah yake kiran wasu mala`iku dashi, wasu ya dunkule su guri daya , wasu kuma ya basu suna daya akan kansu kamar haka:

Sannan a kowane aiki da Allah yake basu yakan kira Mala`iku masu wannan aikin da sunan aikin da suke yi kamar haka:- *Mala`ikun mutuwa *Mala`ikun dake kula da wuta *Mala`ikun ruwan sama *Mala`ikun tsirrai *Mala`ikun da ke kula da kofofin sama *Mala`ikun dake kula da aljanna

Muhallin Mala`iku

[gyara sashe | gyara masomin]

Muhalli na nufin inda mala`iku suke ,ana samun mala`iku a guri kamar haka

Imani da Mala`iku

[gyara sashe | gyara masomin]

Dole ne mutum yayi Imani da Mala`iku dukkan su cewa akwai su kuma basa saba ma Allah akan komai, kuma bayi ne na Allah kuma mutum yayi Imani akan yanda Annabi ya bada labara akansu.

Tabbas mala`iku na rasuwa saidai Allah bai bada labarin yadda yake daukan ransu ba dunkule, amman ya bayar da labarin yanda zai dauki ran Mala`ikan mutuwa bayan kowanne mai rai ya rasu.[10]

Diddigin bayanai na waje

[gyara sashe | gyara masomin]


  1. Dillon, Michael (1999). China's Muslim Hui Community. Curzon. p. 37. ISBN 978-0-7007-1026-3.
  2. Denise Aigle The Mongol Empire between Myth and Reality: Studies in Anthropological History BRILL, 28 October 2014 08033994793.ABA p. 110.
  3. A.C.S. Peacock Early Seljuq History: A New Interpretation Routledge 2013 08033994793.ABA p. 123.
  4. The Encyclopedia of the Arab-Israeli Conflict: A Political, Social and Military History edited by Spencer C. Tucker, Priscilla Mary Roberts p. 917 [1]
  5. The Iraq Effect: The Middle East After the Iraq War By Frederic M. Wehrey p. 91 [2]
  6. Jonathan Brown The Canonization of al-Bukhārī and Muslim: The Formation and Function of the Sunnī Ḥadīth Canon Brill 2007 08033994793.ABA p. 313
  7. Ahmed, Imad-ad-Dean. Signs in the heavens. 2. Amana Publications, 2006. p. 170. Print. 08033994793.ABA
  8. Nicolas Laos The Metaphysics of World Order: A Synthesis of Philosophy, Theology, and Politics Wipf and Stock Publishers 2015 08033994793.ABA p. 177
  9. "Generational Changes in the Leadership of the Ahl-e Sunnat Movement in North India during the Twentieth Century". Archived from the original on 2020-03-17. Retrieved 2019-09-15.
  10. Robert Rabil Salafism in Lebanon: From Apoliticism to Transnational Jihadism Georgetown University Press 2014 08033994793.ABA chapter: "Doctrine"