Man kaɗe

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Man kaɗe
Ebo (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na vegetable fat (en) Fassara
Kayan haɗi sheanut (en) Fassara
Natural product of taxon (en) Fassara Butyrospermum parkii (en) Fassara da kaɗe

Man kade wani mai ne da ya samo asali daga ya'yan bishiyar Kade. Wanda idan aka shanye ya-yan Kaden (tabo) bayan sun nuna to sai a tara ya-yan kaɗen (kwara), bayan ta taru sai ayi amfani da ita.[1][2][3][4] wajen yin Man Kade ta hanyar sarrafa shi don cire man.

mata a Afirka sun kasa man Kade suna sayarwa
man Kade
barzajjiyar kwara kafin a kaishi Nika an shanya ta a rana
wata Mata tana daddaka kwara don yin mankade
mata sun dauko kwara a baho
wajen da akeyin man Kade a Ghana

Yadda ake yin man kade[gyara sashe | gyara masomin]

wata tsohuwa tana yin man Kade
kwara bishiyar kadanya dafaffiya kafin a karasa gyara ta don man Kade
dafaffiyar kwara kafin a kwalbeta. Bayan an kwalbeta sai a shanya ta har ta bushe, sannan a kaita Nika gurin masu injin
mata na baza kwara don shanya ta a rana

Bayan an gama tara qwara, sai a dafa ta sosai bayan an dafa ta sai a sauke ta idan ta huce sai a barta bayan wani dan lokacin kaman sati daya haka tana rana a waje, ko da ana ruwan sama baza ya mata komai ba. Wasu ma suna aje ta bayan an dafa ta tsawon watanni idan bada gaggawa ake sonta ba. Bayan ta sha iska ta saki sai a farfasa a cire bawon mai karfi, Nan ma za'a sake shanya ta a rana nan kam baza a bari ruwa ya jika ta ba. Bayan ta bushe sosai! Sai a barza ta ko a turmi ko a dutse, bayan an gama barza ta sai a kai Nika gurin masu inji na nikan qwara, bayan an niko an dawo ita gida daga nan sai asa ruwa bakin gwargwado man kade yana tasowa ana yade shi. Bayan an gama yade shi a danyen shi sai Kuma a sake soya shi ko kuma narka shi ta yadda zai yi daidai. Daga nan kam sai amfani da shi.

wasu Mata a Afirka suna yin man kaɗe a baho

Amfanin man Kade[gyara sashe | gyara masomin]

Man kade yana da amfani sosai musamman a jikin Dan Adam ana shafa Shi a fata ana kuma shanshi musamman a abinci, amfani Man Kaɗe baya ƙirguwa yana da matukar amfani sosai.

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Mubarak Bala, Muhammad (12 October 2017). "Man Kadanya: Gwamnatin Tarayya ta sanya hannu kan yarjejeniyar dala biliyan 3 da wani kamfani daga Malaysia". legit hausa. Retrieved 1 August 2021.
  2. "Yadda za ku kula da jikinku a lokacin sanyi". bbc hausa. 29 November 2020. Retrieved 25 August 2021.
  3. Sarpong, Akwasi (24 May 2016). "Shea butter in Ghana: Hard labour for smooth skin". bbc news.com. Retrieved 25 August 2021.
  4. "Benin and Burkina Faso: How to Improve Shea Butter Production and Combat Land Degradation". Southsouth Galaxy. 17 March 2019. Retrieved 25 August 2021.