Kaɗe

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kaɗe
Conservation status

Vulnerable (en) Fassara (IUCN 3.1)
Scientific classification
KingdomPlantae
OrderEricales (en) Ericales
DangiSapotaceae (en) Sapotaceae
TribeSapoteae (en) Sapoteae
GenusVitellaria (en) Vitellaria
jinsi Vitellaria paradoxa
C.F.Gaertn.,
Geographic distribution
General information
Tsatso shea wood (en) Fassara da Man kaɗe

Kaɗe ko kuma Kaɗanya sunan Bishiya ce daga cikin bishiyoyi masu ƴaƴa waɗanda ake amfani da su ta hanyar sha da kuma sarrafa su fanni daban-daban. A taƙaice kaɗe bishiya ce mai tarin albarka da amfani don ana shan ƴaƴan sa wato taɓo ana kuma cire mai ta cikin ƙwarar kaɗe (Man kaɗe) ana shan man kaɗe musamman ƙauyuka ana kuma magani dashi da dai sauransu.[1][2]

bishiyar kaɗanya kwantsam da ƴaƴa
bishiyar kaɗe ta yi kakkaɓa ta kuma fantsama fure

Bayani akan Kaɗanya[gyara sashe | gyara masomin]

Bishiyar kaɗe bishiya ce wadda take yin girma sosai don har katako ake yi da ita tanada ganye masu ɗan girma-girma sai kuma tana ƴa'ƴa, ƴa'ƴanta kore ne shar ko yana ɗanye ko nunanne duka ɗaya, abu ɗaya kesa a gane ɗanye da nunanne idan anji ƙamshin sa ko an taɓa da hannu. Saboda shi kaɗe koda ya nuna baya canja kala kamar yadda muka faɗa a baya ana shan kaɗe idan ya nuna mutane da dabbobi tsuntsaye Ɓera da sauransu duk suna amfanuwa da ƴa'ƴan bishiyar kaɗe. Haka masana sun bayyana cewa a cikin ƙwarar kaɗe akwai wani sinadari wanda yake rage ƙiba a turance ana cewa dashi (thin) kaɗe yanada zaƙi, sai dai ba ko wace bishiyar kaɗe keda zaƙi ba. Ƴaƴan kaɗe kafin su nuna sunada bauri idan aka ɗanɗana su (test). Haka kaɗe yana daga cikin bishiyoyi masu kakkaɓa a duk shekara musamman a lokacin rani abinda ake nufi da kakkaɓa anan shine, ganyen bishiya zai zube baki ɗaya sai wani sabo ya tsiro. Shi kaɗai yana daga cikin bishiyoyi waɗanda suna fara fure ne a lokacin da suka fara sabon fure don yin ƴaƴa kaɗe yana fara fure da rani da ƴaƴan duka cikin Bazara yake yinsu sai kuma yana nuna a lokacin ruwan sama duk da cewa baya kaiwa ƙarshen ruwan sama ɗin. Bishiyar kaɗe tsawon ta yakai kusan (82 ft). Bishiyar kaɗe ana samunta ne a ƙasashen Afirka ne kuma a daji ake samun bishiyar kaɗe ko kuma irin cikin gonaki amma kaɗe yafi fitowa a busasshiyar sabana dry Savannah.

Kaɗe ya kwantsama ƴaƴa
ƴaƴan kaɗanya (taɓa)

Ƴaƴan Kaɗe ko Kaɗanya[gyara sashe | gyara masomin]

Bishiyar kaɗe tana fara ƴaƴa ne daga shekara ta goma zuwa sha biyar (10-15years) sai kuma ƴaƴanta suna yawaita a lokacin da kaɗe ya kai shekaru ishirin zuwa talatin (20-30years) kaɗe tana rayuwa har tsawon shekaru ɗari biyu (200years) kuma tana ƴaƴa. Girman ƴaƴan kaɗe suna kai daga santimita 4-8 haka ƴaƴan kaɗe suna wata huɗu zuwa shida kafin su nuna/ƙosa yana yin ƴaƴa da yawa.

dafaffiyar ƙwara kafin a kwalɗeta
an busar da ƙankararriyar ƙwara don yin Man kaɗe

Man kaɗe[gyara sashe | gyara masomin]

Man kaɗe mai ne da ake cirewa daga jikin ƙwarar kaɗe bayan an gama shan taɓo ana amfani dashi sosai musamman Afirka man kaɗe yana ƙunshe da waɗansu sinadarai irin su palmatic, stearic, oleic, linoleic da kuma arachidic. Akwai sinadaran dake sanya ƙiba sosai a mankaɗe.[3]

Ƙasashen da ake samun Kaɗe[gyara sashe | gyara masomin]

Ana samun kaɗe ne a ƙasashe goma sha tara (19) a Afrika ga wasu daga ciki; Najeriya, Ghana, Nijar, Benin, Burkina faso, Kamaru da dai sauransu.[4][5]

Ainihin kalmomin kaɗe[gyara sashe | gyara masomin]

A Najeriya kamar yadda ya gabata Hausawa suna kiran kaɗe da sunaye uku (3) Kaɗe, kaɗanya da kuma taɓo duka sunan kaɗe ne, duk da cewa taɓo yana nufin nunannen kaɗe. Sai kuma da yaren Wolof a ƙasar Senagal suna kiransa da "ghariti" sai ana kiran kaɗe da "bambara" da yaren mutanen ƙasar Mali. Ana kuma kiransa da Okwùmá da yaren Igbo sai da Yoruba ana kiranshi da Òrí.

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Mubarak Bala, Muḥammad (12 October 2017). "Man Kadanya: Gwamnatin Tarayya ta sanya hannu kan yarjejeniyar dala biliyan 3 da wani kamfani daga Malaysia". legit hausa. Retrieved 25 August 2021.
  2. Honfo, Fernande; H. N., Akissoe; Linnemann, Anita; Soumanou Mohamed; Boekel, Martinus (2014). "Nutritional Composition of Shea Products and Chemical Properties of Shea Butter: A Review". Critical Reviews in Food Science and Nutrition. 54 (5): 673–686. doi:10.1080/10408398.2011.604142. S2CID 6345738.
  3. "Yadda za ku kula da jikinku a lokacin sanyi". bbc hausa. 29 November 2020. Retrieved 25 August 2021.
  4. Sarpong, Akwasi (24 May 2016). "Shea butter in Ghana: Hard labour for smooth skin". bbc news.com. Retrieved 25 August 2021.
  5. "Benin and Burkina Faso: How to Improve Shea Butter Production and Combat Land Degradation". Southsouth Galaxy. 17 March 2019. Retrieved 25 August 2021.