Marcel Sabitzer
Marcel Sabitzer an haife shi ne ga 17 a watan Maris ga shekara ta dubu daya da dari tara da tasa'in da hudu (1994) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Austriya wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya a ƙungiyar Premier League Manchester United, ya kasance a matsayin aro ne daga kungiyar Bayern Munich a halin yanzu. Yana wakiltar tawagar kasar Ostiriya . Mafi rinjayen dan wasan tsakiya, Sabitzer na iya taka rawar gani da dama, gami da kai hare-hare, dan wasan tsakiya, mai tsaron gida, mai kai hari da dan wasan gaba na biyu .
Sabitzer ya fara aikinsa na ƙwararren dan kwalo a kasan Austria tare da Admira Wacker da Rapid Wien . Ya koma kulob din RB Leipzig na Jamus a shekara ta 2014 kuma nan da nan aka ba shi aro ga Red Bull Salzburg na kaka daya. Sabitzer ya buga wasanni sama da 200 a kungiyar RB Leipzig, kafin Bayern Munich ta saye shi a watan Agustan a shekara ta dubu biyu da ashirin da daya (2021) kan kudi Yuro miliyan 16.