Marcus Rashford



Marcus Rashford (an haife shi ranar 31 ga watan Oktoba, 1997) dan'wasan kwallon kafa dan kasar Ingila, wanda Dan wasan gaba ne shi a kasar sa da kuma a kungiyarsa ta Manchester United.
Yafara buga wasa a Manchester United tun yana shekara bakwai, ya zura kwallo biyu a wasan sa na farko a kungiyar manchester (wasan da sukayi a gasar UEFA Europa League) bayan raunin da mai buga gaba wato Anthony Martial yasamu), da kuma wasansa na farko a Premier League a watan Febrairu 2016 (da su da Arsenal). Yakuma ci kwallo a wasansa na farko a wasan Manchester derby, da wasan League Cup da kuma a wasansa na farko a UEFA Champions League.






Rashford yaci kwallo a wasansa na farko ma kasarsa England a watan May 2016, wanda yasa yazama mafi karancin shekaru a yan'wasan Ingila da yaci kwallo a wasansa na farko a wasan duniya..
Hotuna
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]|
|
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
|