Martanin Jamus ga Kyoto Protocol

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Jamus ita ce mafi girma a Turai kuma ta 6 mafi girma a duniya, mai fitar da iskar CO2.[1]</link>A cikin Yuli 2007, Jamus tana Turai, tareda mutane miliyan 82.4. Jamus na shigo da mafi yawan kayanta da hanyoyin makamashi, acikin 2004 tana shigo da ganga miliyan 2.135 na mai da biliyan 85.02m³ (2003) na iskar gas a rana. Acikin 2004, Jamus ta fitar da tan miliyan 886 na CO2 . Ac

cikin 2004, akwai kusan motoci miliyan 45 masu rajista a Jamus.

Tsakanin Maris 1998 da Maris 1999, ƙasashe 84 ciki hada Jamus sun sanya hannu kan yarjejeniyar Kyoto. Acikin Maris 2002, Bundestag ya amince da Kyoto baki daya. A watan Mayu na shekara ta 2002, Tarayyar Turai ta gabatar da kasidu na amincewa ga dukkan kasashe 15 da ke cikinta a lokacin.

A matsayinta na kasa ta Annex II, alkawarin da Jamus tayi ga hukumar UNFCCC game da Kyoto shine rage hayaki da kuma samar da turbar tattalin arziki ga kasashe masu tasowa ta hanyar tsaftataccen tsarin raya kasa.

A watan Nuwamba na 2006, rabon da Jamus ta tsara na shekara-shekara shine tan miliyan 482 na CO2.[1] Iskar gas na Greenhouse na Jamus ya ragu da kashi 17.2 cikin 100 daga 1990 zuwa 2004, a cewar UNFCCC. Jamus tana haɓɓaka kuɗaɗen carbon na gwamnati kuma tana tallafawa kuɗaɗen carbon na bangarori daban-daban waɗanda ke da niyyar siyan Kiredit ɗin Carbon daga ƙungiyoyin da ba na Annex I ba. Ƙungiyoyin gwamnati suna aiki kafaɗa da kafaɗa da manyan kayan aiki, makamashi, mai da iskar gas, da kuma ƙungiyoyin sinadarai don ƙoƙarin samun yawancin Takaddun Gas na Greenhouse a cikin arha mai yiwuwa.

Tun lokacin da aka rattaba hannu tareda tabbatar da wannan yarjejeniya, Jamus ta himmatu wajen rage hayakin da take fitarwa zuwa kashi 21 cikin ɗari ƙasa da matakan 1990 tsakanin 2008 da 2012. A watan Nuwamban shekarar 2008, wani bincike ya nuna cewa, Jamus ta riga ta rage fitar da hayaƙi mai gurɓata muhalli da kashi 22.4%, wanda ke nufin ta riga ta kai ga aiwatar da ayyukanta na fitar da hayaƙi na Kyoto.[2]

Wasu daga cikin nasarorin da Jamus ta samu tun bayan sanya hannu kan wannan yarjejeniya[gyara sashe | gyara masomin]

  • Ya zuwa yanzu Jamus ta rage hayakin CO2 da kashi 22.4%.
  • Kasar Jamus ita ce ta kan gaba wajen samar da makamashin iska a duniya tare da injinan iska sama da 16,000, wadanda ke samar da kashi 39% na yawan karfin iska a duniya.
  • Kasar Jamus ta taka muhimmiyar rawa wajen shigar da kashi 64% na karfin samar da makamashin hasken rana a shekarar 2003. 

Jamus ta kuma sanya hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi tare da Isra'ila da Jordan da Masar . An tsara wannan yarjejeniya ne don saukakawa da arha ga ƙasashe masu ci gaban masana'antu irin su Jamus don cimma burinsu na rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli a karkashin wannan yarjejeniya.

Matakai na gaba[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

Hanyoyin haɗi na waje[gyara sashe | gyara masomin]