Jump to content

Masarautar Mutapa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Masarautar Mutapa
Wene we Mutapa (sn)

Wuri
Map
 20°19′S 30°54′E / 20.31°S 30.9°E / -20.31; 30.9
Bayanan tarihi
Mabiyi Masarautar Zimbabwe
Ƙirƙira 1430
Rushewa 1760
Masarautar Mutapa
Samfuri:Native name

Wuri
Map
 20°19′S 30°54′E / 20.31°S 30.9°E / -20.31; 30.9
Bayanan tarihi
Mabiyi Masarautar Zimbabwe
Ƙirƙira 1430
Rushewa 1760

Masarautar Mutapa Wani lokacin ana kiranta daular Mutapa, Mwenemutapa, (Shona, Portuguese)–Masarautar Afirka ce a Zimbabwe, wacce ta faɗaɗa har zuwa ƙasar Mozambik a yau.

Taswirar Fotigal na ƙarni na goma sha shida na Monomotapa yana kwance a cikin kudancin Afirka.

A kalmar Fotigal Monomotapa fassarar sarauta ce ta Shona Mwenemutapa wacce aka samo daga haɗakar kalmomi biyu Mwene ma'ana Yarima ko sarki, da Mutapa ma'ana ƙasa. A tsawon lokaci an yi amfani da laƙabin sarauta ga masarautar gaba ɗaya, kuma ana amfani da ita don nuna yankin masarautar akan taswira daga lokacin.

Akwai labarai na asali na Mutapa da yawa, wanda al'adar baka ta yarda da ita ita ce ta sarakunan Babbar Zimbabwe. Na farko "Mwene" wani jarumi ne mai suna Nyatsimba Mutota daga Masarautar Zimbabwe wanda ya fadada ikon masarautar da farko don gano sabbin hanyoyin gishiri a arewa. [1] An yi imani cewa Yarima Mutota ya sami gishiri a cikin cin nasarar Tavara, wani yanki na Shona. Wani labari na tarihi na asalin daular shine Yarima Mutota ya balle daga kasar Zimbabwe bayan ya yi yaki da yarima Mukwati, (wanda aka yi imanin ko dai dan kaninsa ne ko dan uwansa) ke ikon da mulkin.

Wasu kayayyyakin tarihin masarautar Mutapa, Mwenemutapa

Ɗan Mutota kuma magajinsa, Nyanhewe Matope, ya faɗaɗa wannan sabuwar masarauta zuwa wata daular da ta mamaye yawancin ƙasashe tsakanin Tavara da Tekun Indiya. [2] Wannan daular ta sami nasarar haɗa kan al'ummomi daban-daban a Kudancin Afirka ta hanyar gina dakaru masu karfi da horarwa da karfafawa jihohi gwiwa don shiga tare da ba da damar shiga cikin babbar majalisar daular ga duk wanda ya shiga ba tare da juriya ba.[3] Sojojin Matope sun mamaye masarautar Manyika da kuma masarautun bakin teku na Kiteve da Madanda. [2] A lokacin da Turawan Portugal suka isa gabar tekun Mozambik, Masarautar Mutapa ita ce jiha ta farko a yankin. [2] Ya kafa runduna mai karfi wacce ta mamaye yankin Dande na Tonga da Tavara. Daular ta kai gaci a shekara ta 1480 shekaru 50 kacal bayan ƙirƙirar ta. [4]

Sarkin sarakuna Mutope ya bar daular tare da ingantaccen tsarin addini mai iko. Addinin masarautar Mutapa ya ta'allaka ne da tuntubar ruhohi da na kakannin sarauta. Masu duban ruhohi da aka fi sani da mhondoro sun kula da wuraren ibada a cikin babban birnin ƙasar. Haka kuma mhondoro ya yi aiki a matsayin masana tarihi na baka da ke rubuta sunaye da ayyukan sarakunan da suka gabata. [5]

Baftisma na sarki Siti na Mutapa ta bita na Tomasz Muszyński, 1683, Dominican Monastery a Lublin. João de Mello ya yi bikin baftisma na Siti Kazurukamusapa a ranar 4 ga Agusta 1652, ranar idin St Dominic.
  1. Oliver, page 203
  2. 2.0 2.1 2.2 Oliver, page 204
  3. Williams, Chancellor (1987). The Destruction of Black Civilisation. Chicago: Third World Press. pp. 280. ISBN 9780883780305.
  4. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named :0
  5. Oliver, page 205