Jump to content

Miriam Onuoha

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Miriam Onuoha
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

29 ga Janairu, 2020 -
District: Isiala Mbano/Okigwe/Onuimo
Rayuwa
Haihuwa Najeriya, 18 Satumba 1965 (59 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar jahar Lagos Digiri a kimiyya
Jami'ar Abuja Master of Science (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Princess Miriam Odinaka Onuoha ‘yar siyasa ce ta jam’iyyar All Progressives Congress daga jihar Imo, Najeriya. 'Yar majalisar wakilan Najeriya ce daga mazabar Okigwe ta Arewa.[1] Ta sake samun nasarar zama 'yar majalisar wakilai na tarayya a watan Janairun 2020.[2] An ayyana Obinna Onwubuariri na PDP a matsayin wanda ya lashe zaben na 2019, amma kotun sauraren kararrakin zaben majalisar kasa da ke Owerri a watan Satumbar shekarar 2019, ta kori Obinna Onwubuariri, kuma ta ba da umarnin sake sabon zabe a watan Janairun 2020.[3] Ta sake cin zabe ne bayan kotun sauraren kararrakin zabe da ta zauna a watan Agusta 2020 ta tabbatar da nasararta a zaben watan Janairun 2020.[4]

Farkon Rayuwa da Ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

Princess Miriam ‘yar asalin Umunachi Osu-Ama ce a karamar hukumar Insiala Mbano ta jihar Imo. Ta fara karatun ta na yarinta a Makarantar Central Umunachi Osu-Ama sannan kuma Tilley Gyado College Markudi a jihar Benue. Ta halarci makarantar sakandaren Aquinas Model Osu-Ama kuma a nan ne ta sami shaidar kammala karatun sakandare. Ta ci gaba da karatu a Jami'ar Legas kuma ta kammala karatun digiri a fannin harkokin Gidaje (Estate Management). Ta zarce Jami'ar Abuja inda ta kammala digiri na biyu a kan Tsarin Muhalli da Kariya (Environmental Planning and Protection).[5]

Kafin ta shiga majalisar wakilai ta tarayya, ta yi aiki a matsayin babbar mataimakiya ta musamman ga gwamnan jihar Bayelsa kan Hadin Kan cigaban Kasashen Duniya a tsakanin sauran harkokin siyasa da suka gabata.[6]

  1. "Akinsola, Olanrewaju (26 January 2020). "APC wins Imo rerun election". Today Nigeria. Retrieved 21 November 2020.
  2. "Nseyen, Nsikak (29 January 2020). "Imo: INEC issues Certificate of Return to Miriam Onuoha". Daily Post. Retrieved 21 November 2020.
  3. "Olafusi, Ebunoluwa (18 September 2020). "Tribunal sacks 36-year-old PDP federal lawmaker, orders fresh poll". The Cable. Retrieved 21 November 2020.
  4. "Anonymous (8 August 2020). "Okigwe North: Election tribunal affirms APC Rep. Miriam Onuoha's election". Sun News. Retrieved 21 November 2020.
  5. Anonymous (18 November 2018). "Princess Miriam Onuoha: New Dawn Beckons For Okigwe North". Leadership. Retrieved 21 November 2020.
  6. Anonymous (18 November 2018). "Princess Miriam Onuoha: New Dawn Beckons For Okigwe North". Leadership. Retrieved 21 November 2020.