Mohsen Fakhrizadeh

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mohsen Fakhrizadeh
Rayuwa
Haihuwa Qom, 1958
ƙasa Pahlavi Iran (en) Fassara
Iran
Harshen uwa Farisawa
Mutuwa Absard (en) Fassara, 27 Nuwamba, 2020
Makwanci Imamzadeh Saleh (en) Fassara
Yanayin mutuwa kisan kai (ballistic trauma (en) Fassara)
Karatu
Makaranta Shahid Beheshti University (en) Fassara
Harsuna Farisawa
Sana'a
Sana'a nuclear physicist (en) Fassara
Employers Imam Hossein University (en) Fassara
Kyaututtuka
Aikin soja
Fannin soja Dakarun kare juyin juya halin Musulunci
Digiri brigadier general (en) Fassara
Imani
Addini Shi'a

Mohsen Fakhrizadeh Mahabadi ( Persian: محسن فخری‌زاده مهابادی Fa-Kh-Ree-Zadeh[1] 1958[2] – 27 November shekarar 2020) Cikakken dan kasar Iran ne masanin ilimin kimiyya da Physics. Ana masa inkiya da shugaban masana ilimin gudanar Nukiliya na kasar iran.

An haifeshi a birnin Qom a shekarar 1958, Fakhrizadeh ya shiga Rundunar kare juyin juya hali na musulunci na iran ( Islamic Revolutionary Guard Corps) bayan an tabbatar da tsarin Gwamatin Musulunci a 1979. Yayi karatu a Jami'ar Shahid Beheshti daga bisani kuma ya kammala karatunsa na Doktora a Jami'ar Isfahan. A farkon shekarar 1991 ya zama furofessa na physics a Jami'ar Imam Hossein.

Mohsen Fakhrizadeh
Mohsen Fakhrizadeh

Fakhrizadeh ya jagoranci kungiyar kariya tare da bincike wato Organization of Defensive Innovation and Research tare da wani aiki mai suna Green Salt Project domin inganta ma'adanan uranuyum, kaya masu fashewa da kuma kirkirar sabbin makamai da inganta su. Saboda nasarorin da fakhrizadeh ya samu a ayyukan da ake bashi, hakan yasa ya samu kyakykywan alaka da ayyukan gudanar da makamashin Nukiliya, a dalilin hakan kungiyar UN (United Nation), Kungiyoyin tsaro (Security Council) da kuma gamayyar Amurka suka daskarar da Kadarorin kasar iran a wurin shekarun 2000. A farkon shekarar 2010 ya fara wanzar da ayyukan daya ayyana zai gabatar na kungiyar da yake jagoranta wato kungiyar kariya tare da bincike Organization of Defensive Innovation and Research wanda su kuma Amurka sun kalli wannan yunkuri a matsayin Gudanar da makamashin Nukiliya tare da samar da makaman Nukiliya. Amma su kasar iran a gwamnatan ce ta musanta hakan. Shi kuma prime Minista na Isra'ela cewa yayi fakhrizadeh yaci gaba da aikin da kungiyar IAEA ta haramta wato na samarda makamashin Nukiliya wato AMAD Project . Bayan mutuwar Fakhrizadeh kasar ta girmama Fakhrizadeh inda ta bayyana irin gudunmuwwar daya bada wajen samar da rigakafi na Annobar korona tare da hanyotin magance ta.

A ranar 27 ga watan Nuwamban shekarar 2020, k asar Isra'el ta kashe Mohsen Fajhrizadeh ta hanyar amfani da bindiga mai sarrafa kanta.[3][4] A watab Yunin shekara ta 2021 tsohon shugaban kungiyar leken Asiri ta Isra'el watao Mossad ya bayyana cewa sune suka kashe Fakhrizadeh[5]. Gwamnatin Kasar ta bayyana kisan Fahkrizadeh a matsayin mafi munin Ta'addanci[6], wannan kisan ya tada hankula sosai a yankuna kuma Zauren Dadtawa masu zartarwa a kasar sun tura takarda rufe wani bincike daga kungiyar IAEA akan gudanar da makamashin Nukiliya.

Farkon Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Fakhrizadeh a garin Qom a shekarar 1958, kuma ya kasance daya daga cikin dakaraun kare juyin juya hali na gwamnatin musulunci ta iran a shekarar 1979.

Aikin daya sa gaba[gyara sashe | gyara masomin]

tare da Amir Hatami, Minista na Defens na Jamhuriyar musulunci na iran

A shekarar 1987 Fakhrizadeh yayi digiri na farko akan Bsc Nuclear Physics a Jami'ar Shahid Beheshti.[7] kuma anan ne ya kammala doktora dinshi a fannin nuclear radiation and cosmic rays[8]

A ruwayar gidan yana labarai na Alireza Jafarzadeh, Fakhrizadeh na daya daga membobi na Jami'ar imam Hussaitun farkonn 1991, yana koya karatun Physics.[9][10] A Rahoton da CIA suka bada na shekarar 2007 sun bayyana cewa Matsayi/mukayin fakhrizadeh abune wanda yake a boye[11]

A farkon shekarun 2000, Fakhrizadeh ya jagoranci wani yunkuri/cigaba na samar da Biological Study Centre an siffanta wannan aikin da wata da za'a fadada bincike a ilimin Kimiyya na Physics. kuma wannan bincike anyi shi a wani wuri kusa da Tehran da ake cema Lavizan-Shian.[12]

Mohsen Fakhrizadeh

A shekarar 2020, bayan mutuwar shi Gwamnatin Iran ta ayyana shi a matsayin jigo ta fannin yaki da cutar korona wanda Annobar tayi mummunar barna a kasar ta Iran. A cewar Majid Takht-Ravanchi,

Takunkumin United Nation a (2006-2007)[gyara sashe | gyara masomin]

Kungiyar kariya da bincike (Organization of Defensive Innovation and Research (2011–2020))[gyara sashe | gyara masomin]

Aikin Samar da Makamai na Nukiliya a 2007-2020[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://www.nytimes.com/2021/09/18/world/middleeast/iran-nuclear-fakhrizadeh-assassination-israel.html
  2. https://www.theguardian.com/world/2020/nov/27/mohsen-fakhrizadeh-thought-to-be-key-figure-in-irans-nuclear-efforts
  3. https://www.nytimes.com/2021/09/18/world/middleeast/iran-nuclear-fakhrizadeh-assassination-israel.html?referringSource=articleShare
  4. https://www.inss.org.il/publication/fakhrizadeh/
  5. Peter Beaumont (11 June 2021). "Ex-Mossad chief signals Israel culpability for Iran attacks". The Guardian.
  6. https://www.bbc.com/news/world-middle-east-55111064
  7. https://news.iut.ac.ir/news/30525
  8. https://www.irinn.ir/fa/news/805125/[permanent dead link]
  9. https://www.theguardian.com/world/2020/nov/27/mohsen-fakhrizadeh-iranian-nuclear-scientist-reportedly-shot-dead-near-tehran
  10. https://www.spiegel.de/international/world/the-secret-nuclear-dossier-intelligence-from-tehran-elevates-concern-in-the-west-a-673802.html
  11. https://www.nytimes.com/2020/11/27/world/middleeast/iran-nuclear-scientist-assassinated-mohsen-fakhrizadeh.html
  12. Gaietta 2015, p. 140.