Moussa Konaté (mai wasan ƙwallon ƙafa)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Moussa Konaté (mai wasan ƙwallon ƙafa)
Ɗan Adam
Bayanai
Jinsi namiji
Ƙasar asali Senegal
Country for sport (en) Fassara Senegal
Sunan dangi Konaté
Shekarun haihuwa 3 ga Afirilu, 1993
Wurin haihuwa M'Bour (en) Fassara
Harsuna Faransanci
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Matsayin daya buga/kware a ƙungiya Ataka
Work period (start) (en) Fassara 2011
Wasa ƙwallon ƙafa
Sport number (en) Fassara 14
Participant in (en) Fassara 2012 Summer Olympics (en) Fassara, 2015 Africa Cup of Nations (en) Fassara, 2017 Africa Cup of Nations (en) Fassara da Kofin kwallon kafar duniya ta 2018
hoton musa konate
hoton musa konate

Pape Moussa Konaté[1] (an haife shi a ranar 3 ga watan Afrilun Shekarar 1993), ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Senegal wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan gaba ga ƙungiyar Dinamo Batumi ta Georgia da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Senegal . An kira shi don gasar cin kofin duniya ta FIFA 2018 .[2]

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Farkon aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Moussa Konaté ya fara taka leda a kulob ɗin ASC Toure Kunda de Mbour na kasar Senegal, inda ya taimaka musu wajen samun nasarar zuwa mataki na daya da kuma lashe gasar cin kofin FA na Senegal a kakar wasa ta 2010, wanda ya kai ga buga gasar cin kofin zakarun nahiyoyi na CAF a shekara ta 2011 . A cikin bazarar 2011 Konaté ya tafi Isra'ila na tsawon watanni gwaji tare da Maccabi Tel Aviv. Ya burge kocin Maccabi Moti Ivanir har ya zama ɗan wasa na farko da Maccabi ya ƙulla a kakar 2011–2012.[3][4]

Maccabi Tel Aviv[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan sanya hannu kan kwantiragin shekaru biyu da kulob ɗin, Konaté ya zama ɗan wasa na waje na Maccabi na biyar a cikin tawagar. Ya fara buga wasansa na farko a gasar cin kofin zakarun Turai ta UEFA Europa League zagaye na biyu da FK Khazar Lankaran inda ya zura ƙwallo ta farko tare da taimakawa Eliran Atar ta biyu a nasarar Maccabi da ci 3-1.[5]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Uefa Profile Moussa". UEFA.
  2. "2018 FIFA World Cup: List of players" (PDF). FIFA. 15 July 2018. p. 26. Archived from the original (PDF) on 19 June 2018. Retrieved 15 July 2018.
  3. "Maccabi Tel Aviv recruit Senegal's Moussa Konaté". Goal.com. 13 June 2011. Retrieved 18 August 2012.
  4. "M. Konaté". Soccerway. Retrieved 26 November 2016.
  5. "UEFA Europa League 2011/12 - History - M. Tel-Aviv-Xäzär Länkäran –". Uefa.com. 14 July 2011. Retrieved 18 August 2012.