Muhammad Inuwa
Muhammad Inuwa | |||
---|---|---|---|
1963 - 22 Oktoba 1963 ← Muhammadu Sanusi I - Ado Bayero → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 1904 | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Mutuwa | 1963 | ||
Ƴan uwa | |||
Mahaifi | Muhammad Abbass | ||
Sana'a |
Muhammadu Inuwa shi ne Sarkin Kano, da ya maye gurbin Sarki Muhammadu Sanusi na 1 wanda ya sauka a shekarar 1963. An maye gurbin Sarki Muhammadu Inuwa da Sarki Ado Bayero ɗan ɗan'uwansa kuma surukinsa. [1]
Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Inuwa a shekara ta 1904 miladiya ga dangin Muhammad Abbass, wanda a lokacin shi ne Sarkin Kano. Mahaifinsa ya rasu yana da shekara goma sha biyar kuma daga baya aka sanya shi a hannun dan uwansa Abdullahi Bayero. Lokacin da Bayero ya hau kan mukamin sarki a shekarar 1926, ya naɗa Inuwa a matsayin Turakin Kano kuma ya naɗa shi Hakimin Ungogo. Ya zama Hakimin Minjibir a shekarar 1932. A shekarar 1939, ya gaji dan uwansa Abdulkadir dan Abbas a matsayin Galadiman Kano kuma aka naɗa shi hakimin Dawakin Kudu. Inuwa ya tasirantu da darikar Tijjaniyya Shaihu Yahya b. Muhammad Naffakh kuma an ɗauke shi da tsoron Allah a tsakanin takwarorinsa da kuma mai hakuri. [2] A shekarar 1944, ya kasance kansila a Hukumar Yan asalin Kano kuma daga shekarar 1952 zuwa shekara ta 1963, ya kasance ɗan majalisar yankin Arewa. Ya riga ya tsufa lokacin da ya zama Sarkin Kano a shekarar 1963, Muhammadu Inuwa ya gaji ɗan ɗan'uwansa Sanusi a watan Afrilun shekarar 1963, dukkansu sun yi takarar neman sarki a shekarar 1953. Ya yi mulki na wata uku kawai kafin ya rasu.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Paden, J. N. (1973). Religion and political culture in Kano. Berkeley: University of California Press. p233
- ↑ "Sarkin Kano Muhammadu Inuwa (1963)". Archived from the original on 2016-11-11. Retrieved 2021-05-20.