Muhammadu Bello Kagara

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Muhammadu Bello Kagara dan Mallam Shaihu Usman ne, mahaifinsa shine Alkalin Alkalan Kagara, na farko. Shi Malam Shehu dan Mallam Muhammadu Badamasi ne Hakimin Nufawa a Unguwan Taku Birnin Sokoto.

Haihuwa[gyara sashe | Gyara masomin]

An haife shi a Kagara a shekarar 1889, ya rayu tsawon shekarar 82.[1]

Karatu[gyara sashe | Gyara masomin]

Kagara yayi makarantar Dan-Hausa ta Kano wacce makaranta ce wanda turawan mulkin mallaka suka fara kafawa a Arewa. Inda daga bisani aka turasu Garu Ruwa domin fara karantarwa a sauran lardin.[1]

Rayuwa[gyara sashe | Gyara masomin]

An tura Bello Kagara makarantar Zaria saboda kwazonsa. Saboda kokarinsa na shiga gari gari dan neman ilimi bai bar zaria ba saida aka fara kiranshi Mallam. Daga nan aka bude makarantar Tirenin a Kwaleji a Katsina (Barewa Kwalej) inda aka dauko shi domin ya karantar da addini musulunci da larabci. Da aka bude ‘Medical Class’ inda aka fara karantar da famasi sai aka mayar dashi can ya cigaba da koyar da lissafi.Yayi karantarwa a makarantar IHSI–ETC watau makarantar koyawa Malaman Elementary Ilimin Malanta.

Alkalanci[gyara sashe | Gyara masomin]

Bayan an maida shi kwaleji anan Sarki Alhaji Muhammad Dikko ya gane zurfin iliminsa ya gane anfaninsa sai ya bukaci abashi shi don ya shiga dashi cikin majalisar sa. Hakan bai yiwu ba sai bayan yayi ritaya a watan Maris, 1945. Sai Sarkin Katsina Alhaji Usman Nagogo ya nada shi Karamin Alkali. Bayan rasuwar Babban Alkali aka nada shi Babba Alkali. Alhaji Bello yayi rubuce rubuce da dama shine ya wallafa mashahurin littafin nan ‘Gandoki’ kuma shine ya wallafa littafin ‘Sarkin Katsina’. Ya samu lambobin girma a rayuwarsa har guda uku. Ta karshen itace M.B.E. mutum ne mai hakuri.

Mutuwa[gyara sashe | Gyara masomin]

Allah yayiwa Bello Kagara rasuwa a ranar Lahadi 21 ga watan nuwanba 1971. Ya rasu yana da shekara 82 a duniya.[1]

Bibiliyo[gyara sashe | Gyara masomin]

  • Bobboyi, H., Yakubu, Mahmud.(2006). The Sokoto Caliphate: history and legacies, 1804-2004, 1st Ed. Kaduna, Nigeria:Arewa House. ISBN 978-135-166-7
  • Hamman, Mahmoud, 1950- (2007). The Middle Benue region and the Sokoto Jihad, 1812-1869 : the impact of the establishment of the Emirate of Muri. Kaduna: Arewa House, Ahmadu Bello University. ISBN 978-125-085-2. OCLC 238787986.
  • Usman Muhammad Bugaje. The Tradition of Tajdeed in West Africa: An Overview International Seminar on Intellectual Tradition in the Sokoto Caliphate & Borno. Center for Islamic Studies, University of Sokoto (June 1987)
  • Hugh A.S. Johnston . Fulani Empire of Sokoto. Oxford: 1967. ISBN 0-19-215428-1.
  • S. J. Hogben and A. H. M. Kirk-Greene, The Emirates of Northern Nigeria, Oxford: 1966.
  • Muhammad Bello Kagara. Sarkin Katsina. ISBN:978169209

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 1.2 Muhammad Bello Kagara. Sarkin Katsina. p.p 246-247 ISBN:978169209