Musa Babayo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Musa Babayo
Rayuwa
Haihuwa Azare, 21 ga Maris, 1957 (66 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan kasuwa da ɗan siyasa

Musa Babayo (an haife shi a ranar 21 ga watan Maris a shekara ta alif 1957) ma'aikacin banki ne na Nijeriya, dan kasuwa, kuma dan siyasa,sannan marubuci ne kuma dattijon ƙasa ne wanda ya kasance Sakataren Kasa na Kwamitin Ayyukan Jam'iyyar PDP a mataki na Kasa daga shekara ta 2012 zuwa shekara ta 2015 kafin shigarsa All Progressives Congress (APC) a ranar 15 ga watan Oktoban shekarar 2015. Ya kasance Mataimakin Sakataren Jam’iyyar na kasa daga shekara ta 2008 zuwa shekara ta 2011 kafin daga baya ya zama Sakataren Jam’iyyar na Kasa.

Tarihin Rayuwa da Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Musa kuma ya girma a garin Azare, karamar hukumar Katagum,a jihar Bauchi. Ya halarci makarantar firamare ta Nasarawa ta Yamma,a Azare, a shekara ta 1965-1972 sannan ya tafi makarantar sakandaren gwamnati ta Katagum, a Azare daga 1972 zuwa 1976. Ya kuma halarci Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda ya yi karatun Digirinsa na farko a fannin mulki, harkar banki da kuma harkokin kudi. Ya kuma tafi Makarantar Kasuwanci ta Manchester, Birtaniya wadda aka kafa don manyan masu karatun harkar Banki, a watan Yunin 1993, ya kuma yi Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Wales (UWIST), Birtaniya don digiri na biyu a fannin fasaha da alkintawa, 1984.

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

A tsakanin harkokin siyasarsa, Babayo ya rike ofisoshi daban daban na gwamnati da masu zaman kansu. A matsayin sa na babban ma'aikacin gwamnati, kuma ya kasance Shugaban Asusun Tallafawa Ilimi kuma shugaban kwamitin amintattu TETFund.[ana buƙatar hujja]

A matsayin sa na shugaban Asusun Tallafa Ilimi na Manyan Makarantu (TETFund), Babayo ya gudanar da sauyin da ya haifar da soke Dokar Haraji ta shekarar 1998 da maye gurbin ta da dokar TetFund ta watan Yulin 2011. .

Harkar Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Wallafe-Wallafe[gyara sashe | gyara masomin]

Shine marubucin littafin mai taken diflomasiyyar tattalin arziki da kuma manufofin kasashen waje na Najeriya wanda aka fara bugawa a shekara ta 2015.

Lambobin Yabo[gyara sashe | gyara masomin]

Sarkin masarautar Bauchi, Suleiman Adamu ne ya ba Babayo mukamin Talban Katagum a ranar 13 ga Janairun 1996. Har ila yau, an ba shi lambar yabo ta Babban Jami'in Harkokin Kiwon Lafiyar Jama'a ta Kungiyar Kula da Isarwa mai zaman kanta ISDMG, 2014.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]