Jump to content

Mutuwaren Taurari

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
mutuwaren taurari
astronomical object type (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na massive compact halo object (en) Fassara
Yana haddasa Hawking radiation (en) Fassara
Karatun ta astrophysics (en) Fassara
Has characteristic (en) Fassara Tolman–Oppenheimer–Volkoff limit (en) Fassara, gravitational wave (en) Fassara, nauyi, electric charge (en) Fassara da angular momentum (en) Fassara
Hannun riga da white hole (en) Fassara

Makabartar Taurari ko (black hole a Turanci), masana kimiyya sun kira ramin da sunan Black Hole, amma wani marubuci cikin harshen Hausa, a wani rubutunsa da ya yi a shafin BBC Hausa ya kira shi da Bakin Rami ko Mutuwaren Taurari, a fassara mara yanci, kamar yadda ya fadi (Karanta mukalar a nan). Amma a wannan makalar an yi masa lakabi da Makabartar Taurari ne sakamakon shi wani katon rami ne mai girman gaske wanda masana kimiyya suka ce shi ne wajen da taurari ke fadawa ko kasancewa bayan wa'adin rayuwarsu.

Girman ramin ya kai kilomita biliyan daya, wanda girmansa ya fi duniyarmu sau miliyan uku, wanda kuma masana suka kira shi "dodo". Ramin Black Hole din yana nesa daga duniya da kilomita triliyan 500, na'urar Telescope guda takwas suka dauki hoton daga duniyarmu.

Na'urar Event Horizon Telescope (EHT) ne ya dauki hoton, manyan na'urorin hangen nesa na telescope takwas ne suka dauki hoton. Masanan sunce an samu damar daukar hoton ramin black hole ne a duniyar M87.

Black Hole Tauraro ne?

[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 1939 wannan babban masanin Kimiyyar wato Albert Einstein da kuma nazariyyarsa ta "General theory of relativity" ya rubuta cewa babu yadda maganadisun janyowa (gravity) zai iya janyo taurari saboda akwai iya matakin da wasu abubuwan ba za su matsu ba. Yana nufin cewa babu ta yadda tauraro mai tsananin nauyi zai iya faduwa saboda ya fi karfin "gravity" ya yi tasarrufi da shi. Masana Kimiyya duk sun yarda da Einstein har sai da wani masanin Kimiyya dan asalin Amurka wato John Wheeler ya bayyana cewa kuskure ne.

Ya fadi cewa akwai wani guri da a yanzu ake kira "black hole" da yake janyo irin wadannan taurari cikinsa. Wannan tauraro da yake fadawa wannan guri shi aka fara kira da "frozen star" (daskararren tauraro). A "black hole" akan samu tarayyar wadannan dokoki ne guri guda, don haka ake zaton tun da an kasa hade wadannan dokoki to idan aka fahimci "black hole" to za a iya hadesu.

Wannan shi ne abin da Stephen Hawking ya karar da rayuwarsa akai amma har ya mutu a shekarar da ta gabata bai samu nasara ba! Stephen Hawking yana cewa mafi kankantar "black hole" yana da nauyin babban tsaunin dutse a wannan duniya tamu. Amma an fi samun manyan da suka ninninka rana nauyi. Kada ka manta rana ta ninka wannan duniyar da muke kai nauyi ninkin-ba-ninkin. Hoton "black hole" din da aka dauko a ranar Alhamis ya yi nauyin rana sau sama da biliyan shida.