Nafi' al-Madani

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Nafi' al-Madani
Rayuwa
Haihuwa Madinah, 689
ƙasa Umayyad Caliphate (en) Fassara
Daular Abbasiyyah
Mutuwa Madinah, 785
Malamai Abu Ja'far al-Madani (en) Fassara
Abd al-Rahman ibn Húrmuz (en) Fassara
Shayba ibn Nassah (en) Fassara
Q56365452 Fassara
Ɗalibai
Sana'a
Sana'a Malamin akida, qāriʾ (en) Fassara, muhaddith (en) Fassara da mufassir (en) Fassara
Imani
Addini Musulunci
Mabiya Sunnah

Abu Ruwaym Ibn Abd ʽ -Rahman Ibn Abi Na ʽ im al-Laythi ( Larabci: أبو رويم بن عبدالرحمن بن أبي النعيم الليثي‎ (70-169AH), wanda aka fi sani da Nafi ʽ al-Madani, yana daya daga cikin masu watsa Qira'at guda bakwai, ko hanyoyin karatun Alqur'ani . [1] A wajen kasar Masar, tsarin karatun Alkur'ani shi ne mafi shahara a nahiyar Afirka gaba daya, kuma isnadinsa na komawa ga sahabban Annabi Muhammad (SAW) ya tabbata.

An haifi Nafi ʽ a shekara ta 689 CE, kuma ya rasu a shekara ta 785 miladiyya. Iyalinsa mutanen Isfahan ne, ko da yake shi kansa an haife shi kuma ya rasu a Madina .

Hanyar karatunsa ta hanyar fitattun dalibansa guda biyu, Qalun da Warsh, ita ce yanayin karatun kur'ani da aka fi amfani da shi a Arewacin Afirka, Yammacin Afirka da Qatar . Yana da jimillar masu watsa littafai guda hudu na karatunsa; Baya ga Qalun da Warsh, ya kuma mika karatunsa ga Isma'il bin Ja'afar al-Ansari da Ishaq bin Muhammad al-Musayyabi. [2] Salon karatun Nafi ya shahara har ya wuce na malamansa na Madina.

Ƙira'a[gyara sashe | gyara masomin]

Magana[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Muhammad Ghoniem and MSM Saifullah, The Ten Readers & Their Transmitters. (c) Islamic Awareness. Updated January 8, 2002; accessed April 11, 2016.
  2. Shady Nasser, Canonization, p. 135.