Natalya Vasko

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Natalya Vasko
Rayuwa
Haihuwa Chervonohrad (en) Fassara, 19 Oktoba 1972 (51 shekaru)
ƙasa Ukraniya
Kungiyar Sobiyet
Karatu
Makaranta National University of Theatre, Film and TV in Kyiv (en) Fassara 1994)
Sana'a
Sana'a Jarumi
Kyaututtuka
IMDb nm4689622

Natalya Lubomyrivna Vasko [lower-alpha 1] (an haife ta a ranar 19 ga watan Oktoban shekarar 1972) yar wasan kwaikwayo ce ta kasar Ukraine kuma mai gabatar da wasan talabijin. Daga 1999 zuwa 2019, ta kasance babbar yar wasan kwaikwayo na Kyiv National Academic Molodyy Theater. Ta lashe lambar yabo ta Golden Dzyga a cikin "Best Support Actress" a cikin fim din The Nest of the Turtledove (2017).[1] Ita ma memba ce ta Ukrainian Film Academy.[2]

Tarihin Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Vasko a ranar 19 ga watan Oktoban shekarar 1972 a Chervonohrad, yankin Lviv . A lokacin 'yammatancinta, ta tsunduma a cikin wasan kwaikwayo na yara "Fairytale", inda ta rawa a kwaikwayo iri iri, kama daga gimbiya zuwa azzaluma. Bayan makaranta, a karo na biyu, ta shiga Kyiv National IK Karpenko-Kary Theatre, Cinema da Television University a yayinda ta kammala karatunta a 1994. Daga aji na 4, ta yi wasa a Kyiv Acaemic Theatre of Drama and Comedy . Daga 1999 zuwa 2019, ta kasance babbar yar wasan kwaikwayo na Kyiv National Academic Molodyy Theater. [3]

A 2008, Vasko ta ɗauki nauyin wasan kwaikwayo na "Morning with Inter" a tashar TV ta Ukrainian Inter .

Rayuwarta[gyara sashe | gyara masomin]

Daga aurenta na farko, Vasko tana da 'ya Yulia (b. 1997).[4][5] A ranar 28 ga Fabrairu, 2022, lokacin da Rasha ta mamaye Ukraine, Vasko ta auri Andriy Shestov, wanda ta kasance tare tsawon shekaru takwas da suka gabata.[6]

Bayanan kula[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. “Золота Дзиґа»: оголошено переможців першого українського Оскара" (in Ukrainian). Maximum.fm кіноакадемії. 21 April 2017. Archived from the original on 23 February 2022. Retrieved 21 April 2017.
  2. ^ Сергій ВАСИЛЬЄВ, Віталій ЖЕЖЕРА 25 Молодих історій. Ювілейне ревю (2005)
  3. Сергій ВАСИЛЬЄВ, Віталій ЖЕЖЕРА 25 Молодих історій. Ювілейне ревю (2005)
  4. Наталя Васько на порталі «Кіно-театр»". Archived from the original on 13 February 2020. Retrieved 13 February 2020.
  5. "Наталя Васько на «Телепорталі»". Archived from the original on 13 February 2020. Retrieved 13 February 2020.
  6. У цей вирішальний час боротьби за незалежність від рашистської навали»: Наталія Васько повінчалася зі своїм обранцем". «Ukrainska Pravda» (in Ukrainian). Archived from the original on 9 March 2022. Retrieved 2022-02-28.

Hanyoyin haɗi na waje[gyara sashe | gyara masomin]