Neena Gill
Neena Gill | |||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
2 ga Yuli, 2019 - 31 ga Janairu, 2020 District: West Midlands (en) Election: 2019 European Parliament election (en)
1 ga Yuli, 2014 - 1 ga Yuli, 2019 District: West Midlands (en) Election: 2014 European Parliament election (en)
20 ga Yuli, 2004 - 13 ga Yuli, 2009 District: West Midlands (en) Election: 2004 European Parliament election (en)
20 ga Yuli, 1999 - 19 ga Yuli, 2004 District: West Midlands (en) Election: 1999 European Parliament election (en) | |||||||||
Rayuwa | |||||||||
Haihuwa | Ludhiana (en) , 24 Disamba 1956 (67 shekaru) | ||||||||
ƙasa | Birtaniya | ||||||||
Harshen uwa | Turanci | ||||||||
Karatu | |||||||||
Makaranta | Liverpool John Moores University (en) | ||||||||
Harsuna | Turanci | ||||||||
Sana'a | |||||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||||
Wurin aiki | Strasbourg da City of Brussels (en) | ||||||||
Kyaututtuka | |||||||||
Imani | |||||||||
Jam'iyar siyasa | Labour Party (en) |
Neena Gill, CBE 'yar siyasa ce ta Jam'iyyar Labour na Burtaniya. Ta yi aiki a matsayin memba na Majalisar Tarayyar Turai (MEP) na West Midlands da farko daga shekarar 1999 zuwa 2009, sannan bisani daga 2014 zuwa 2020.
Kuruciya da aiki
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Gill a Ludhiana, Punjab, Indiya.[1] Ta yi hijira zuwa Ƙasar Ingila (Birtaniya) tare da danginta a lokacin tana da shekaru goma. Mahaifinta dan kasuwa ne.[2] Gill ta fara aiki ne a ɗakin karatu a lokacin tana da shekara 16.[3] Ta kammala karatun digirnta na farko a fannin nazarin zamantakewa daga Jami'ar Liverpool John Moores a shekara ta 1979. Ta kasance mataimakiyar shugabar kungiyar dalibai.[4] Daga baya Gill ta sami digiri na biyu na ƙwararru daga Cibiyar Hadaka na. Gidaje wato Chartered Institute of Housing a shekara ta 1984 kuma a cikin shekara ta 1996, ta kammala babban shirin gudanarwa a Makarantar Kasuwancin London.[4]
Bayan kammala karatunta, Gill ta zama akawu mai horarwa amma ta yi aiki na tsawon makonni shida kafin ta tafi ta zama jami'ar gidaje a Ealing Borough Council.[5] Tana da shekaru 29, Gill ta zama shugabar kungiyar ASRA, inda ta zama mace ta farko, wacce ba farar fata ba kuma mafi karancin shekaru a kungiyar gidaje ta Burtaniya.[2][5] Daga nan ta yi aiki a matsayin shugabar rukunin gidaje na Newlon.[4]
Majalisar Turai
[gyara sashe | gyara masomin]Kafin nasarar zaben Labour na ahekarar 1997, Gill ta yi aiki tare da mambobin majalisar ministocin Labour don taimakawa wajen bunkasa manufofin zamantakewar jam'iyyar.[2] A shekara ta 1999, an zabe ta a matsayin mace ta farko a Asiya MEP a Majalisar Turai.[6] Wakilin Yammacin Midlands tsakanin shekara ta 1999 da 2009, Gill ya rike mukamai daban-daban, ciki har da Shugaban Wakilin Hulda da Jama'a tare da Indiya da Shugaban Wakilin Hulda da Kasashen Kudancin Asiya da SAARC. Ta kuma kasance memba a kwamitin harkokin shari'a da kuma kwamitin kasafin kudi.
Gill ba ta yi nasara a yunkurinta na sake fitowa zabe a karo na uku a matsayin MEP a shekara ta 2009.[7] A lokacin zamanta a wajen majalisa, ta yi aiki a matsayin mataimakiyar shugaban kasa kan harkokin kamfanoni (Turai da Asiya Pacific) na kamfanin software SAS.[8][9]
A shekara ta 2014 ne, aka sake zaɓan ta a matsayin ɗaya daga cikin MEPs na Labour guda biyu (ɗayan kuma Siôn Simon ) na West Midlands.[10] A wannan wa'adin, ta kasance mamba a kwamitin tattalin arziki da harkokin kudi, kwamiti na musamman kan hukunce-hukuncen haraji, laifukan kudi, kaucewa biyan haraji da gujewa, kuma wani bangare na tawagar hulda da Indiya da Amurka.[11] Ta kasance mai himma musamman kan ka'idojin kuɗi kuma ita ce mai ba da rahoto ga Dokokin Kasuwancin Kuɗi na Turai (MMF) na 2015.[4]
A shekarar 2017 ne, Gill ta kasance ɗaya daga cikin masu nasara biyu na Burtaniya (ɗayan kuma shine MP na Conservative Priti Patel ) na Pravasi Bharatiya Samman, babbar girmamawa da gwamnatin Indiya ta baiwa NRIs.[12] A cikin wannan shekarar, an nada ta Kwamandan Order of the British Empire (CBE) a cikin 2017 Sabuwar Shekara Karrama.[13] A cikin Yuli 2018, Gill ya zama ɗan'uwan girmamawa na Jami'ar Liverpool John Moores.[5]
An sake zaben ta a zaben 2019 na 'yan majalisar Turai a matsayin MEP na Labour na West Midlands.[14] Gill ta kasance memba a kwamitin tattalin arziki da harkokin kudi. A watan Satumba na 2019, Gill ta shiga cikin tawagar don dangantaka da Japan a matsayin Shugaba da Majalisar Haɗin Kan Majalissar ACP-EU a matsayin Mataimakin Shugaban da S&D Co-Coordinator.[15]
Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Ta auri Dr. John Towner, mai ba da shawara kan muhalli, a 1982 kuma suna da ɗa guda. Sun rabu a 2009.[1][2]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 "Gill, Neena". UK Who's Who. Retrieved 17 September 2019.
- ↑ 2.0 2.1 2.2 2.3 "One of a kind". Politico. 2 April 2003. Retrieved 17 September 2019.
- ↑ "5 questions with... Neena Gill". The Parliament Magazine. 3 May 2017. Retrieved 17 September2019.
- ↑ 4.0 4.1 4.2 4.3 "Johnson, Steve (23 November 2014). "Political animal stalks EU money funds". Financial Times. Retrieved 17 September 2019.
- ↑ 5.0 5.1 5.2 "Honorary Fellow Neena Gill CBE". Liverpool John Moores University. 13 July 2018. Retrieved 17 September 2019.
- ↑ "Harman's office Thatcher U-turn". BBC News. 16 September 2009. Retrieved 17 September 2019.
- ↑ "European elections 2009: West Midlands region". The Daily Telegraph. 26 May 2009. Retrieved 17 September 2019.
- ↑ "Neena Gill, Member of European Parliament for the West Midlands (Labour)". University of Warwick. Retrieved 17 September 2019.
- ↑ "Neena Gill". Women Economic Forum. Retrieved 17 September 2019.
- ↑ "West Midlands". BBC News. Retrieved 17 September 2019.
- ↑ 8th parliamentary term". European Parliament. Retrieved 17 September 2019.
- ↑ "Pravasi Bharatiya Samman Awards-2017". Ministry of External Affairs. 9 January 2017. Retrieved 17 September 2019.
- ↑ "New Year's Honours 2017: CSV". gov.uk. 30 December 2016. Retrieved 17 September 2019.
- ↑ "European election 2019: Brexit Party tops West Midlands polls". BC News. 27 May 2019. Retrieved 17 September 2019.
- ↑ "9th parliamentary term". European Parliament. Retrieved 17 September 2019.