Novatus Dismas

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Novatus Dismas
Rayuwa
Haihuwa Tanga (en) Fassara da Arusha (en) Fassara, 2 Satumba 2002 (21 shekaru)
ƙasa Tanzaniya
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
S.V. Zulte Waregem (en) Fassara1 ga Yuli, 2022-
 

Novatus Dismas Miroshi (an haife shi a 2 ga watan Satumba 2002), ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Tanzaniya wanda ke taka leda a ƙungiyar ƙasa ta Tanzaniya.[1]

Ya buga wasan kasa da kasa tare da tawagar 'yan kasa da shekaru 20 ta Tanzaniya a ranar 16 ga Fabrairu 2021 da Ghana da ke fafatawa a gasar cin kofin Afrika na 'yan kasa da shekaru 20 da aka yi a Mauritania a ci 4-0.[2]

A ranar 19 ga watan Fabrairu, 2021, Dismas ya ci wa Tanzania kwallonsa ta farko a ragar Gambia a wasan da suka tashi 1-1.[3]

A ranar 2 ga watan Satumba 2021, ya fara buga babban wasansa na farko da Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA a 2022 a kunnen doki 1-1.[4]

A ranar 7 ga watan Satumba, 2021, Dismas ya ci wa Tanzania babbar kwallo ta farko a ragar Madagascar a wasan neman tikitin shiga gasar da ci 3-2.[5]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Tanzania-N. Dismas Miroshi - Profile with news, career statistics and history - Soccerway". us.soccerway.com . Retrieved 2021-09-11.
  2. "Tanzania-N. Dismas Miroshi-Profile with news, career statistics and history - Soccerway". us.soccerway.com . Retrieved 2021-09-11.
  3. Tanzania-N. Dismas Miroshi-Profile with news, career statistics and history - Soccerway". us.soccerway.com . Retrieved 2021-09-11.
  4. "FIFA". fifa.com. Retrieved 2021-09-11.
  5. "FIFA". fifa.com. Retrieved 2021-09-11.