Jump to content

Nura Hussain

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Nura Hussain Tsohon jarumi ne a masana'antar fim ta Hausa wato kannywood, ya Dade Yana fim ya Yi zamani tare dasu Ibrahim. maishinku, ubale Wanke Wanke, sani danja, Aminu Ahlan,Yana yawan fitowa a malami. natsatsen mutum ne a fili har a fina finan shi, ya daukaka a sanadiyyar fim din BAYAJIDDA da yayi, labarin tarihi. Sannan Kuma shi furodusa ne. A bangaren siyasa Kuma a mulkin tsohon shugaban kasa buhari ya nada Jarumin a matsayin [1]kwamishina na alhazai.[2]

Takaitaccen Tarihin Sa[gyara sashe | gyara masomin]

Nura Hussain shine Cikakken sunan sa furodusa ne Africa tv, TV show host, Dan siyasa ne kuma. An haifeshi a ranar 15 ga watan mayu shekarar alif dari tara da saba'in da takwas (1978A.C) a quarters din yakasai a municipal a garin Kano . Mahaifin sa malamin addini ne malam Hussain da matarsa Malama ummu _kulthum muhammad , shine yaro na uku a cikin Yara Sha biyu da mahaifin sa ya haifa. Yana yawan fitowa a ya sayyadi ya bude makarantar islamiyya tashi Mai suna, ansarul Islam a yakasai inda take kunshe da dalibai sama da 400, shi kansa malamin addini ne wanda yake karantarwa, a makarantar islamiyya da gida.

Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

Nura yayi karatun firamare a yolawa Islamic school daga shekarar alif dari tara da tamanin da daya (1981) zuwa alif dari tara da tamanin da biyu (1982),daga Nan ya shiga shahuci judicial Islamic school inda yayi karatun firamare bayan ya baro yolawa, daga shekarar 1982 zuwa 1991, daga Nan ya shiga wawure makarantar junior sakandiri school daga shekarar ta alif 1992 zuwa 1995, daga Nan ya shiga government Arabic teachers college gwale inda yayi karatun sakandiri yayi shekara daya a makarantar, ya tafi makarantar Alliya senior secondary school inda ya karasa karatun sakandiri a shekarar alif dari tara da casa'in da biyar (1995) zuwa alif dari tara da casa'in da bakwai (1997). Daga Nan ya shiga school of legal studies Kano inda yayi difloma a bangaren civil law daga shekarar 2000 zuwa 2003.[3]mutum ne mai ilimin zamani dana islama.

Fara fim[gyara sashe | gyara masomin]

Nura ya fara fim ne a shekarar alif 1997 ya fara da fitaccen fim Mai suna "zarge" inda ya fito a suna ya sayyadi saboda girmamawa da furodusas ke masa. Yayi fina finai da dama daga Nan yazo ya fara fim nashi inda ya zama furodusa a masana'antar. Ya fara son fim ne daga sanda ya kalla fim Mai suna "Kara da kiyashi" ganin yadda jaruman suka fadakar, sati biyu da kallan fim din yaje tauraruwa drama a court road yaje ya shiga.daga Nan auwalu muhammad sabo furodusa na sarauniya fim ya kirasa ye mishi tayin fim inda ya amsa bisa yarjewar iyayensa shine fim din sa na farko Wanda yayi da jaruma margayiya hauwa Ali dodo,dag nan ya fito a fim Mai suna linzami da wuta SE Kuma fim din sangaya. Yana da kamfani Mai suna N.H . production inda yayi Wani fim Mai suna"lokaci" shi yayi furodusin yakuma fito a fim din, daga Nan SE fim din harsashe, farin wata, akalla yayi furodusin fina fina sui Kai 200. Jarumin ya boye na wasu shekaru daga baya kuma ya dawo yana lekowa a masana'antar

Aure[gyara sashe | gyara masomin]

nura nada matar aure guda daya , Mai suna Aisha bello bagudu sunyi aure a watan mayu 12 ga watan a shekarar 2003, a yanzun haka suna da Yara bakwai a duniya hudu mata uku Maza.

Fina finan sa

  • Zarge
  • BAYAJIDDA
  • lokaci
  • Farin wata
  • Wafati
  • Sangaya
  • Limzami da wuta
  • Da kishiyar gida
  • Halin mutum jarin sa[4] da sauran su.
  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-29. Retrieved 2023-07-29.
  2. https://aminiya.ng/mahaifin-jarumi-nura-hussaini-ya-rasu/
  3. https://hausa.legit.ng/1281321-da-duminsa-buhari-ya-nada-jarumin-kannywood-nura-hussain-a-matsayin-kwamishinan-hukumar-alhazan-najeriya.html
  4. http://hausafilms.tv/actor/nura_hussain