Jump to content

Ogbonna Nwuke

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ogbonna Nwuke
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

Rayuwa
Haihuwa Omuma, 16 Satumba 1959 (65 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar jihar Riba s
Sana'a
Sana'a civil servant (en) Fassara
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Ogbonna nwuke (an haife shi a ranar 16 ga watan Satumba 1959) ɗan siyasan Najeriya ne, mawallafin jarida kuma mamallakin Port Harcourt Telegraph. Ya yi aiki a ma’aikatun gwamnati da ba zaɓaɓɓu ba da kuma zaɓaɓɓu, ciki har da Daraktan Hulɗa da Yaɗa Labarai na Gwamna Chibuike Amaechi, Kwamishinan Watsa Labarai da Sadarwa (2008-2009) da Kasuwanci da Masana’antu (2009-2010) da kuma ɗan Majalisar Dokoki ta Tarayya. mai Wakiltar mazaɓar Etche-Omuma (2011-2015).[1]

Rayuwar farko

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Ogbonna nwuke a ranar 16 ga watan Satumba 1959 ga dangin nwuke a ƙaramar hukumar Omuma, jihar Ribas. Mahaifinsa JHE ya kasance sakataren harkokin cikin gida na majalisar dokoki a ƙarƙashin gwamnatin Nnamdi Azikiwe a Gabashin Najeriya, daga bisani kwamishinan lardin Fatakwal kuma ƙaramin ministan ayyuka a ƙarƙashin gwamnatin MI Okpara.[2]

Aikin siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

An zaɓi nwuke a matsayin ɗan majalisar wakilan Najeriya a shekarar 2011. Ya wakilci mazaɓar tarayya Etche-Omuma har zuwa shekara ta 2015.[3]

  • Jerin mutanen jihar Ribas
  1. Odimegwu Onwumere (19 January 2011). "Ogbonna Nwuke: A Publisher heading to polish House of Representatives". Nigerian Voice. Retrieved 15 October 2016.
  2. "The story of Port Harcourt city". Vanguard. Port Harcourt. 18 October 2016. Retrieved 15 October 2016.
  3. Jimitota Onoyume; Davies Iheamnachor (15 March 2016). "My people will enjoy good representation — Nwuke". Vanguard. Port Harcourt. Retrieved 15 October 2016.