Okokomaiko Wani yanki ne a cikin garin Ojo, wanda ke cikin jihar Legas a kudu maso yammacin Najeriya, a kan hanyar Legas zuwa Badagry.[1][2][3] Gwamnatin jihar Legas karkashin jagorancin tsohon gwamna Akinwunmi Ambode ta fadada mahimmancin wannan hanyar a yankin yammacin Afirka tare da shirin fadada hanyar Legas zuwa Badagry zuwa hanyar mota biyu. An fara ginin ne daga Eric Moore zuwa Okokomaiko.[4] Ambode, a lokacin da yake rike da mukamin gwamna, ya yi maraba da duk wani mai saka hannun jari da ke son haɗa kai da gwamnatin jihar wajen aikin gina titin mil 2 a Badagry, wanda ya hada da yankin Okokomako. Ya ce a halin yanzu an fara aiki daga Eric More zuwa Okokomaiko amma a shirye muke mu haɗa gwiwa da duk wani mai saka jari da ke son fara aikin kasha na biyu wanda shi ne hanya na 10 daga Okokomaico zuwa Seme Border.[5]