Olayide Adelami
Olayide Adelami | |||
---|---|---|---|
ga Faburairu, 2024 - | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Ondo, | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Kwalejin Kimiyya da Fasaha, Ibadan Jami'ar jahar Lagos Jami'ar Olabisi Onabanjo | ||
Harsuna | Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da accountant (en) | ||
Wurin aiki | Jahar Ondo | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Olayide Owolabi Adelami (an haife shi a ranar 3 ga watan Afrilu 1958) ɗan siyasan Najeriya ne wanda ya zama mataimakin gwamnan jihar Ondo tun a ranar 1 ga watan Fabrairu 2024.[1][2] Ya taɓa zama mataimakin magatakarda na Majalisar Dokoki ta ƙasa.
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Adelami a Owo, Jihar Ondo, Najeriya. Ya yi karatun firamare a St. Francis Catholic Primary School, sannan ya ci gaba a Kwalejin Imade da ke Owo. Ya sami takardar shaidar matakin GCE A daga The Polytechnic, Ibadan. Adelami ya samu digirin sa na BSc a fannin harkokin kasuwanci a jami'ar Legas, inda ya yi digirinsa ( Masters) a irin wannan kwas a jami'ar jihar Ogun, sannan ya yi digirin digirgir a fannin tsaro da dabarun bincike daga jami'ar jihar Nasarawa.[3]
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Adelami ya yi aiki a matsayin akawu a watan Disamba 1983, a Hukumar Ma'aikata ta Tarayya. Daga shekarun 1996 zuwa 2000, an naɗa shi a manyan ofisoshi ciki har da babban asibitin ƙasa, Abuja. [3] [4]
Adelami ya zama shugaban sashin kuɗi da asusu na majalisar tarayya a jihar Ondo har zuwa shekarar 2007, inda aka naɗa shi darakta. Ya yi babban kwas na gudanarwa daidai kwas na 54 a Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabarun Ƙasa a shekarar 2008. A shekarar 2014, Adelami ya samu muƙamin babban sakatare na hukumar saye da sayarwa, gidaje da ayyuka, rawar da ya taka har zuwa lokacin da aka naɗa shi a matsayin mataimakin magatakarda na majalisar dokoki ta ƙasa (Nigeria).[5][6]
Adelami ya fara aikin siyasa na cikakken lokaci a shekarar 2018, a ƙarƙashin jam'iyyar All Progressives Congress. Gwamna Lucky Aiyedatiwa ne ya naɗa shi mataimakin gwamnan jihar Ondo a ranar 24 ga watan Janairun 2024, sannan kuma ya rantsar da shi a ranar 1 ga watan Fabrairu 2024. [4]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Ojomo, Olufemi. "Olaide Adelami Sworn In As Ondo Deputy Governor". Channels TV. Retrieved 31 May 2024.
- ↑ Tope, Fayehun (1 February 2024). "Adelami Sworn In As Ondo Deputy Gov, Promises 100% Loyalty To Aiyedatiwa". Leadership. Retrieved 31 May 2024.
- ↑ 3.0 3.1 Kayode, Oyero. "Aiyedatiwa Nominates Ex-NASS Clerk Adelami As Deputy". Channels TV. Retrieved 31 May 2024. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":0" defined multiple times with different content - ↑ 4.0 4.1 "Adelami becomes deputy governor to Aiyedatiwa". 2 February 2024. Retrieved 14 September 2024. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name "ondo" defined multiple times with different content - ↑ Ojomo, Olufemi. "Olaide Adelami Sworn In As Ondo Deputy Governor". Channels TV. Retrieved 31 May 2024.
- ↑ Tope, Fayehun (1 February 2024). "Adelami Sworn In As Ondo Deputy Gov, Promises 100% Loyalty To Aiyedatiwa". Leadership. Retrieved 31 May 2024.