Olu Ginuwa
Appearance
Olu Ginuwa | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a |
Olu Ginuwa (wanda aka fi sani da Iginuwa ) sarkin Itsekiri ne wanda shine Olu na Warri na farko. [1] Shi ne ɗan fari na Oba Olua, Oba na 14 na Benin (1473-1480 AD) kuma magaji ga sarautar Babbar Masarautar Benin. Ya yi hijira daga Masarautar Benin aka naɗa shi Olu na Warri na farko. Ya yi mulki na tsawon shekara 30. Ya yi sarauta daga 1480 zuwa 1510. Sai ɗansa Olu Ijijen (Ogbowuru) ya gaje shi. Wani daga cikin ƴaƴansa, Olu Irame ya zama sarki bayan Olu Ijijen. [2] [3]
Nassoshi
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Arrivedo". arrivedo.com. Retrieved 9 May 2020.[permanent dead link]
- ↑ "Place Of Ijala In Warri Kingdom: History, Development". The Pointer News Online. Retrieved 9 May 2020.[permanent dead link]
- ↑ "Itsekiri | people". Britannica. Retrieved 9 May 2020.