Jump to content

Onikan Stadium

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Onikan Stadium
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin Najeriyajahar Lagos
BirniLagos,
Coordinates 6°26′33″N 3°24′08″E / 6.44247°N 3.40219°E / 6.44247; 3.40219
Map
History and use
Wasa ƙwallon ƙafa
Occupant (en) Fassara Stationery Stores F.C. (en) Fassara
Ikorodu City F.C. (en) Fassara
Sporting Lagos F.C. (en) Fassara
Maximum capacity (en) Fassara 10,000

Filin wasa na Mobolaji Johnson Arena [1] filin wasa ne mai amfani da yawa a Legas. A halin yanzu ana amfani da shi don wasan ƙwallon ƙafa kuma filin wasa ne na ƙungiyoyi daban-daban na Legas, musamman Ikorodu United FC, Stationery Stores FC, First Bank da Julius Berger FC. Filin wasan yana daukar mutane 10,000 kuma shine mafi dadewa a Najeriya. Filin wasan wanda yake a kusurwar kudu maso gabashin Legas Island kusa da dandalin Tafewa Balewa, an gina asalin filin wasan ne a shekarar 1930 kuma bayan shekaru shida an sanya masa sunan Sarki George V. A tsakanin 1963 zuwa 1973, an san shi da sunan filin wasa na birnin Legas. An gyara filin wasa na Onikan na yanzu tare da bude shi don ayyukan kwallon kafa da al'adu a shekarun 1980. A watan Maris na 2008, Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya ta dakatar da filin wasan don amfani da sauran wasannin kakar wasa lokacin da wani hari da aka kai wa kungiyar Warri Wolves ya jikkata da dama bayan sun tashi babu ci da First Bank.

Onikan stadium

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]