Orogbu Obiageli

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Orogbu Obiageli
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Nnamdi Azikiwe University (en) Fassara
Harsuna Turanci
Harshen Ibo
Sana'a
Sana'a malamin jami'a, ɗan siyasa da Malami
Employers Nnamdi Azikiwe University (en) Fassara

Farfesa Lilian Obiageli Orogbu ’yar Najeriya ce kuma ‘yar siyasa.[1] Tana ɗaya daga cikin mata 17 kacal da aka zaɓa a majalisar dokokin ƙasar ta 10. An zaɓe ta a majalisar wakilai ta tarayya daga yankin Awka North/Awka South Federal Constituency na jihar Anambra akan tikitin jam’iyyar Labour Party, LP.

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Lilian Orogbu farfesa ce a fannin kasuwanci a jami'ar Nnamdi Azikiwe Awka. An zaɓe ta a Majalisar Wakilai ta 10 daga Mazaɓar Tarayya ta Awka North/Awka ta Kudu a ranar 25 ga watan Fabrairu 2023 akan tikitin LP. Ta samu kuri'u 34,713 inda ta doke manyan abokan hamayyarta, ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA, Obi Nwankwo wanda ya samu kuri'u 24,814, da ɗan takarar jam'iyyar People's Democratic Party, PDP Emeka Igwe wanda ya samu kuri'u 21,850.[2] Orogbu na ɗaya daga cikin mata 17 kacal da aka zaɓa a majalisar dokoki ta ƙasa ta 10 mai mambobi 469 da suka haɗa da majalisar dattawa da ta wakilai.[3][4]


Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Obarayese, Sikiru (2023-02-28). "#ElectionResults2023: Unizik lecturer wins Awka North/South Federal Constituency for Labour Party". Tribune Online (in Turanci). Retrieved 2023-05-01.
  2. Ozoji, Raymond (March 1, 2023). "Opposition Elements Attempted To Falsify [[Awka ta Arewa|Awka]]-North, South Election Results – Orogbu". Retrieved May 1, 2023. URL–wikilink conflict (help)
  3. Sule, Itodo Daniel (2023-03-11). "Meet the 17 women who made it to 10th National Assembly". Daily Trust (in Turanci). Retrieved 2023-05-01.
  4. "DID YOU KNOW? Women got only 3.5% of national assembly seats declared so far". TheCable (in Turanci). 2023-03-09. Retrieved 2023-05-01.