Othman Ladan Baƙi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Othman Ladan Baƙi
Rayuwa
Haihuwa 1927
Mutuwa 2008
Sana'a

Othman Ladan Baki (an haife shi a shekara ta alif 1927), ɗa ne ga Kankia Muhammad Sada Nadada, kuma jikan Sarkin Katsina Muhammadu Dikko. Ya kasance mai kula da Sashen Ayyuka da Ruwan yankunan Karkara a Karamar Hukumar Katsina a shekarar alif 1960. Ladan ya kasance mamba a majalisar dokoki ta Arewa daga shekarar alif 1952, zuwa alif 1956 kuma an sake zabe a shekarar alif 1956. Ya kasance sakataren majalisa a ma'aikatar ciniki da masana'antu daga shekara ta alif 1955 zuwa shekara ta alif 1956, sannan ya zama ministan kasuwanci na Arewacin Najeriya a shekara ta alif 1965, sannan ya zama kwamishinan lardunan Zaria daga shekara ta alif 1962 zuwa shekarar alif 1965.[1][2] A shekarar alif 1982 aka nada Dr. Othman Ladan-Baki, OFR a matsayin Shugaban Hukumar Hidima ta Majalisar Dokoki ta Kasa.[3]

Ƙuruciya da Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Ladan a shekarar alif 1927, a cikin garin Katsina ta tsohuwar jihar Kaduna, ga dangin Kankiya Muhammad Sada Nadada. Ya yi karatu a Katsina Elementary School, Katsina Middle School, Kaduna College da Cvil Engineering School, Kaduna, sannan ya halarci horar wa akan Civil Engineering a Biritaniya daga shekara ta alif 1959 zuwa shekarar alif 1960.[1]

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Ladan gogaggen injiniya ne kuma ɗan siyasa. Ya kasance mai kula da ayyuka a karamar hukumar Katsina a shekarar alif 1956, sannan kuma ya zama kansilan ayyuka da bincike da samar da ruwan sha a karkara (Works, Survey and Rural Water Supply) a shekarar alif 1960, kafin ya zama kwamishinan lardi na Zariya daga shekara ta alif 1962 zuwa shekarar alif 1965. Ladan ya kasance mamba a majalisar dokokin Arewa daga shekara ta alif 1952 zuwa shekarar alif 1956, kuma an sake zabe a shekara ta alif 1956. Ya kasance sakataren majalisa a ma'aikatar ciniki da masana'antu daga shekara ta alif 1955 zuwa shekarar alif 1956, sannan ya zama ministan kasuwanci na Arewacin Najeriya a shekara ta alif 1965, sannan ya zama kwamishinan lardunan Zaria daga shekarar alif 1962 zuwa shekarar alif 1965. [4] A shekarar alif 1982 aka nada Dr. Othman Ladan-Baki, OFR a matsayin Shugaban Hukumar Hidima ta Majalisar Dokoki ta Kasa. Ya rike manyan mukamai da dama a nan kamar: Shugaban Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Katsina a watan Nuwamba, shekara ta alif 1987; Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya a shekarar alif 1989; Yayin da a cikin shekara ta alif 1991, an nada shi memba Emirate Council. Ya kasance Gwamna, Cibiyar Shari'a ta Kasa; A watan Agusta, shekara ta alif 1998, aka nada shi Asa Kwamishina a Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).

Kyaututtuka da karramawa[gyara sashe | gyara masomin]

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ba Baki lambar yabo na OFR a shekarar alif 1964, don karramawa da sadaukarwar da ya yi wajen yi wa kasa hidima. Daga baya a cikin shekarar alif 1976, ABU Zaria ta ba shi digirin digirgir a fannin shari'a (LLB).

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 "Admin (2016-11-02). "LADAN-BAKI, Alhaji (DR.) Othman". Biographical Legacy and Research Foundation. Retrieved 2022-06-22.
  2. "Ibrahim, Lawal (26 June 2008). "Nigeria: Ladan Baki, Wife Die in Auto Crash". allAfrica. Retrieved 22 June 2022.
  3. "Chronology | Federation Civil Service Commission". www.fedcivilservice.gov.ng. Retrieved 2022-06-22.
  4. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named :0