Ousseini Tinni
Ousseini Tinni | |||||
---|---|---|---|---|---|
25 ga Maris, 2016 - 23 ga Maris, 2021
| |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Tinoma (en) , 10 Disamba 1954 (70 shekaru) | ||||
ƙasa | Nijar | ||||
Karatu | |||||
Harsuna | Faransanci | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | Nigerien Party for Democracy and Socialism |
Ousseini Tinni (an haife shi ne a ranar 10 ga watang Disamban shekarar 1954) ɗan siyasan Nijar ne na Jam’iyyar Nijar don Demokraɗiyya da Gurguzu . Ya kasance shugaban majalisar kasa tun 25 ga Maris din shekarar 2016.
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Tinni a Tinoma, a cikin Yankin Dosso . Ya tafi makarantar sakandare a Marseille, Faransa, kuma daga baya ya halarci Ecole Supérieure et des Techniques Economiques a Lomé, Togo. Daga baya Tinni yayi aiki a matsayin ma'aikacin gwamnati a ma'aikatu da sassan gwamnati da dama.
A zaben watan Fabrairun 2016, an zabe shi ga Majalisar Dokoki ta kasa a matsayin dan takarar PNDS. A ranar 25 ga Maris 2016 an zabe shi Shugaban Majalisar Dokoki ta Kasa da kuri’u 109 cikin kuri’u 118 da ke goyon baya. Wakilan adawa sun kauracewa zaben.