Jump to content

Patricia Ofori

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Patricia Ofori
Rayuwa
Haihuwa Huntsville (en) Fassara, 9 ga Yuni, 1981
ƙasa Tarayyar Amurka
Mutuwa Huntsville (en) Fassara, 20 ga Afirilu, 2011
Karatu
Makaranta Alabama Agricultural and Mechanical University (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Ghana women's national football team (en) Fassara2003-2007
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya
Tsayi 1.7 m

Patricia Ofori (an haife ta a ranar tara 9 ga watan Yuni, shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da tamanin da ɗaya 1981 zuwa ashirin 20 ga watan Afrilu, shekarar alif dubu biyu da goma sha ɗaya 2011) ƴar wasan ƙwallon ƙafa ce ta ƙasar Ghana wacce ta taka leda a matsayin mai tsaron gida. Ta kasance memba na Kungiyar mata ta kasar Ghana .

Rayuwa ta farko

[gyara sashe | gyara masomin]

Ofori ta girma ne a Accra .

Ayyukan ƙwaleji

[gyara sashe | gyara masomin]

Ofori ta halarci Jami'ar Alabama A&M a Amurka. [1]

Ayyukan kulob ɗin

[gyara sashe | gyara masomin]

Ofori ta buga wa Mawuena Ladies a Ghana.

Ayyukan ƙasa da ƙasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Ofori ta kasance memba na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta ƙasar Ghana daga shekarar alif dubu biyu da uku 2003 zuwa shekara ta alif dubu biyu da bakwai 2007. Ta kasance ɗaya daga cikin tawagar a gasar cin kofin duniya ta mata ta FIFA ta shekarar alif dubu biyu da ukku 2003 da kuma gasar cin kocin duniya ta mata na FIFA ta shekara ta alif dubu biyu da bakwai 2007.

Ofori ta mutu a ranar 20 ga Afrilun shekara ta dubu biyu da goma sha ɗaya 2011 a sanadiyar hatsarin mota. [2]Ford Mustang dinta ta yi karo da Toyota Tacoma a wurin haɗuwa da Patterson Lane da Pulaski Pike a yankin Meridianville. [3] an binne ta ne a Accra, Ghana a ƙarshen Afrilun shekara 2011. [1]

  • Jerin 'yan wasan kwallon kafa na mata na kasa da kasa na Ghana
  1. "List of Players" (PDF). FIFA Women's World Cup China 2007. FIFA. 2007. Archived from the original (PDF) on October 14, 2012. Retrieved 2007-09-28.
  2. "1 dead, 1 injured in Madison County wreck".
  3. "Patricia Ofori's Obituary on The Huntsville Times".